DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 89

Shugaba Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya wajen inganta horo da walwar jami’an tsaro

0

Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da goyon bayan gwamnati ga ‘yan sanda ta hanyar ingantaccen horo, kayan aiki, da jin dadin ma’aikata, tare da magance tushen rashin tsaro ta ci-gaban tattalin arziki, a yayin bikin kammala horon sabbin ‘yan sanda 1,001 a makarantar horon ‘yan sanda da ke a Wudil, Kano.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya ce sabbin jami’an suna da alhakin girmama hakkin bil’adama, gudanar da aiki cikin gaskiya, da kare doka yayin da suke shiga aiki a fagen tsaron cikin gida.

Kwamandan POLAC, AIG Patrick Atayero, ya bayyana cewa ‘yan sandan da aka yaye din sun sami cikakken horo na ilimi da aikin aiki, kuma cibiya na ci-gaba da fadada shirye-shirye da inganta gine-gine domin daidaita aikin ‘yan sanda da matakan kasa da kasa.

SERAP ta maka Akpabio da Abbas kotu bisa zargi kasa bayyana yadda aka kashe Naira biliyan 18 na kudin majalisa

0

Kungiyar SERAP ta shigar da ƙara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, bisa zargin rashin bayyana yadda aka kashe ₦18.6bn da aka ware domin ginin ofishin hukumar kula da ayyukan majalisa (NASC).

SERAP ta shigar da ƙarar ne a makon da ya gabata, inda aka ambaci Akpabio da Abbas a madadin dukkan ’yan majalisar, tare da sanya NASC a matsayin mai amsa ƙara.

A cewar sanarwar da mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar ranar Lahadi, ƙarar ta biyo bayan munanan zarge-zarge da ke cikin rahoton mai duba asusun kuɗi na tarayya na 2022, wanda aka wallafa a 9 ga watan Satumba 2025.

SERAP ta ce rahoton ya nuna NASC ta biya fiye da ₦11.6bn ga wani kamfani da ba a bayyana ba domin ginin sabon ofishinta cikin watanni 24, inda kuma aka ce an ƙawata kwangilar da fiye da ₦6.9bn a wani canji da aka yi ba tare da tsarin daukar kwangila ba.

Kungiyar ta kara da cewa an bayar da kwangilolin ne ba tare da tantance bukata, tallar jarida, yin gasa, kwangila ta rubuce ko amincewar Majalisar Zartaswa ta Tarayya, haka kuma babu takardar ‘No Objection’ daga Hukumar BPP.

Rundunar sojin saman Nijeriya ta ragargaji mabuyar’yan ta’adda a jihohin Borno da Katsina

0

Rundunar sojin saman Nijeriya sun samu manyan nasarori a ayyukan su na kai farmaki, inda suka tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda a jihar Katsina sannan suka dakile hare-haren ‘yan tada kayar baya a Chibok, Borno.

Wannan ya biyo bayan amfani da bayanan leken asiri da ya bai wa jiragen yakin damar kai farmaki daidai-wa-daida kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A Katsina, farmaki na farko da aka kai da karfe 6 na safe ya hallaka masu ta’addanci da suka yi yunkurin tserewa daga sansanonin su a Kankara, Faskari da Malumfashi, yayin da farmaki na biyu a Danfako ya rusa cibiyoyin kayan aiki da sansanonin masu ta’addanci. Wannan ya raunana kungiyar sosai kuma ya hana su motsi cikin ‘yanci a Yammacin Arewacin Nijeriya

A Borno kuwa, jiragen saman sun tallafa wa sojojin Birget na 28 yayin da ‘yan ta’adda suka kai hari mai fadi a Chibok.

An kai farmaki hudu kan ‘yan ta’addan da ke tattara kansu ko ja da baya, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da hana su sake shirya hari. Wannan hadin gwiwar aiki na kasa da sama ya tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Kungiyar Miyetti Allah ta yi alkawarin aiki hannu da hannu da jami’an tsaro a jihar Kaduna

0

Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN) reshen Kudancin Kaduna ta bayyana aniyar haɗa kai da hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a yankin.

Wannan kudiri ya fito ne a taron da aka gudanar a Kafanchan, hedkwatar karamar hukumar Jema’a, a ranar Lahadi.

Shugaban MACBAN na yankin Kudancin Kaduna, Alhaji Mato Yahaya, ya ce lokaci ya yi da za a nemo mafita, tare da yin kira ga shugabanni su faɗi gaskiya kuma su gabatar da shawarwari masu amfani domin magance matsalolin yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin makiyaya da sauran al’umma.

A nasa jawabin, shugaban MACBAN na jihar Kaduna, Alhaji Abdulhamid Albarka, ya ce an shirya taron ne domin tattara ra’ayoyin jagororin Fulani na ƙananun hukumomi, sannan a mika su ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace.

Rundunar sojin Nijeriya ta ceto mutane 7 da aka sace a jihar Kano

0

Sojojin Operation MESA ƙarƙashin Birget ta 3 sun ceto mutane bakwai da ’yan bindiga suka sace a Tsanyawa, bayan samun kiran gaggawa daga Yankamaye Cikin Gari a daren Juma’a.

Jami’an tsaro sun isa wurin cikin gaggawa tare da rundunar sojin sama da ’yan sanda, suka yi artabu da maharan inda suka kubutar da wadanda aka sace.

Sanarwar da Kyaftin Babatunde Zubairu ya fitar ta ce maharan sun kashe wata mata mai shekaru 60 kafin isowar sojoji. Bayan musayar wuta, rundunar ta bi sawun ’yan bindigar zuwa hanyar Rimaye, inda suka sake cakumar juna har maharan suka tsere suka bar mutanen da suka sace.

Sai dai mutum huɗu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ba a same su ba tukuna, yayin da rahoton ya ce ’yan bindigar sun tsere zuwa yankin Kankiya a jihar Katsina. Jami’an tsaro suna ci-gaba da bin diddigin motsin su domin gano su.

Kwamandan Birget ta 3 ya yaba da jajircewar sojoji, yana kuma kira ga jama’a da su cigaba da bayar da sahihan bayanai don ƙarfafa yaki da ’yan bindiga a yankunan kan iyaka.

Babu al’ummar da za ta ci-gaba ba tare da bin doka da adalci ba – Gwamnan Kano

0

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jaddada cewa babu ci-gaba a kowace al’umma idan ba a gina mulki kan doka, adalci da gaskiya ba.

Gwamnan ya faɗi haka a yayin taron karramawa na CREED, inda aka ba shi lambar yabo ta Gwamnan Shekara.

A madadinsa, Babban Lauyan Jihar Kano, Abdulkarim Maude (SAN), ya ce gwamnatinsu ta gudanar da gyare-gyare domin rage jinkirin shari’a da matsalolin tsare-tsaren da suka daɗe ba tare da gurfanarwa ba.

Haka kuma ya bayyana cewa an gano wasu mutane da suka shafe shekaru a tsare ba tare da fayil ko lauya ba, lamarin da ya sa gwamnan ya umarci a nemo takardun, a gaggauta shawarwarin shari’a, a gurfanar da inda ya dace, ko a janye inda adalci ya buƙaci hakan.

Gwamnan ya ce ana faɗaɗa taimakon shari’a da haɗa masu aiki na sa-kai don tabbatar da cewa adalci bai taɓa dogaro da kuɗi ko matsayi ba. Manufarsa ita ce ganin tsarin shari’a ya zama mai sauƙin samu, ingantacce kuma adalci ga kowa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kebbi ya gana da shugaba Tinubu bayan ceto daliban da aka sace a jihar Kebbi

0

Shugaba Bola Tinubu ya karɓi Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, a fadar shugaban Nijeriya Abuja, inda suka tattauna kan ayyukan tsaro a Arewa maso Yamma da ceto ɗalibai ’yan makarantar GGCSS Maga da aka sace a ranar 17 ga watan Nuwamba.

Gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu bisa umarnin gaggawa da kuma yadda hukumomin tsaro da leƙen asiri na tarayya suka samu nasarar ceto ɗaliban a ranar 26 ga watan Nuwamba, kafin a miƙa su ga iyayensu a Birnin Kebbi. Ya kuma yaba wa ministan tsaro, Bello Matawalle, bisa jagorantar aikin ceton.

Taron ya zo ne a lokacin da ake fama da sake ƙaruwa da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, musamman hare-haren da ke nufi a makarantu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar ADC tsagin Atiku na duba yiwuwar daukar Peter Obi ko Amaechi a matsayin ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027

0

Jam’iyyar ADC bangaren Atiku Abubakar ya fara neman ɗan takarar mataimaki daga Kudu domin zaben 2027, inda ake duba yiwuwar daukar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi. Idan Obi ya ƙi amincewa, ana sa ran Atiku zai koma ga tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi.

Dele Momodu, abokin siyasar Atiku, ya ce haɗin gwiwar Atiku da Obi ita ce mafi ƙarfi wajen kalubalantar shugaba Bola Tinubu, yana tunasar da cewa sun taba yin tikitin tare a 2019 kafin su yi takara dabam a 2023.

Momodu ya dora laifin rashin haɗin kan su kan wasu magoya bayan Obi, yana mai cewa babu ’yan siyasa daga Kudu kaɗai da za su iya kayar da Tinubu. Ya ce tuni ya sha yi wa Obi magana cewa ya yi gaggawar rungumar wannan dama ko kuma Atiku ya koma ga Amaechi, wanda ya ce yana da ƙwarewar siyasa sosai.

Hakazalika, ya gargadi Obi cewa jinkiri na iya jawo masa rasa babbar dama a 2027, yana mai cewa Atiku bai da lokaci wajen jira kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ni ne Kirista mafi matsayi a wannan gwamnati – Akpabio

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya ce shi ne babban jami’in Kirista mafi matsayi a gwamnatin Nijeriya, yana mai danganta nasararsa ta siyasa ga “ni’imar Allah ta musamman.”

Akpabio ya faɗi haka ne a lokacin bude wani wajen ibada na Regina Coeli a Uyo, kamar yadda sanarwar mai taimaka masa, Jackson Udom, ta tabbatar.

A cewarsa, tafiyarsa daga rashin sani zuwa zama mutum na uku a jagorancin ƙasa hujja ce ta yadda Allah ke ɗaukaka wandanda ya nufa. Ya ce duk Kirista na iya samun irin wannan tagomashi muddin ya tanadi kansa don albarkar Ubangiji.

Ya kuma jaddada muhimmancin aikin ikilisiya, yana cewa ko gudummawar da ta kai kobo goma ga aikin gina coci tana da lada mai girma.

Har ila yau, jaridar Punch ta ruwaito Akpabio ya bayyana shirinsa na gina sabon wurin ibada a cikin majalisar dokoki na Abuja.

‘Yan bindiga sun sace matafiya a babban titin jihar Kogi

0

Wasu ’yan bindiga sun tare motoci a kan hanyar Isanlu–Makutu–Idofin da ke Yagba ta Gabas a jihar Kogi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Mazauna wajen sun ce maharan sun kafa shinge na tsawon sa’o’i, inda motoci uku suka faɗa tarkonsu, kuma mutum ɗaya kacal ya kuɓuta.

Kamar yadda mazauna yankin suka shaida, jami’an soji da ’yan sa-kai sun bi sawun maharan daga baya suka kuma yi musayar wuta da su, lamarin da ya kai ga kubutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka sace.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP William Aya, ya ce mutum biyu aka sace yayin da wani Raji Adesukami ya tsere, kuma an tura tawaga ta musamman domin ceto sauran.

Wata majiya ta rundunar soji ta bayyana cewa sojojin Birget ta 12 sun ceto mutane biyar a yayin wani samame da suka kai a yankin Isanlu–Egbe a ranar 29 ga Nuwamba, bayan wasu hare-haren sace mutane da suka afku a yankin.

A halin yanzu, Gwamna Usman Ododo ya ce za a kai farmaki kai tsaye cikin dazukan da ’yan bindiga ke ɓoyewa domin kare rayukan jama’ar jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.