DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 90

Jam’iyyar ADC tsagin Atiku na duba yiwuwar daukar Peter Obi ko Amaechi a matsayin ‘yan takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2027

0

Jam’iyyar ADC bangaren Atiku Abubakar ya fara neman ɗan takarar mataimaki daga Kudu domin zaben 2027, inda ake duba yiwuwar daukar tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi. Idan Obi ya ƙi amincewa, ana sa ran Atiku zai koma ga tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi.

Dele Momodu, abokin siyasar Atiku, ya ce haɗin gwiwar Atiku da Obi ita ce mafi ƙarfi wajen kalubalantar shugaba Bola Tinubu, yana tunasar da cewa sun taba yin tikitin tare a 2019 kafin su yi takara dabam a 2023.

Momodu ya dora laifin rashin haɗin kan su kan wasu magoya bayan Obi, yana mai cewa babu ’yan siyasa daga Kudu kaɗai da za su iya kayar da Tinubu. Ya ce tuni ya sha yi wa Obi magana cewa ya yi gaggawar rungumar wannan dama ko kuma Atiku ya koma ga Amaechi, wanda ya ce yana da ƙwarewar siyasa sosai.

Hakazalika, ya gargadi Obi cewa jinkiri na iya jawo masa rasa babbar dama a 2027, yana mai cewa Atiku bai da lokaci wajen jira kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ni ne Kirista mafi matsayi a wannan gwamnati – Akpabio

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya ce shi ne babban jami’in Kirista mafi matsayi a gwamnatin Nijeriya, yana mai danganta nasararsa ta siyasa ga “ni’imar Allah ta musamman.”

Akpabio ya faɗi haka ne a lokacin bude wani wajen ibada na Regina Coeli a Uyo, kamar yadda sanarwar mai taimaka masa, Jackson Udom, ta tabbatar.

A cewarsa, tafiyarsa daga rashin sani zuwa zama mutum na uku a jagorancin ƙasa hujja ce ta yadda Allah ke ɗaukaka wandanda ya nufa. Ya ce duk Kirista na iya samun irin wannan tagomashi muddin ya tanadi kansa don albarkar Ubangiji.

Ya kuma jaddada muhimmancin aikin ikilisiya, yana cewa ko gudummawar da ta kai kobo goma ga aikin gina coci tana da lada mai girma.

Har ila yau, jaridar Punch ta ruwaito Akpabio ya bayyana shirinsa na gina sabon wurin ibada a cikin majalisar dokoki na Abuja.

‘Yan bindiga sun sace matafiya a babban titin jihar Kogi

0

Wasu ’yan bindiga sun tare motoci a kan hanyar Isanlu–Makutu–Idofin da ke Yagba ta Gabas a jihar Kogi, inda suka yi garkuwa da matafiya da dama.

Mazauna wajen sun ce maharan sun kafa shinge na tsawon sa’o’i, inda motoci uku suka faɗa tarkonsu, kuma mutum ɗaya kacal ya kuɓuta.

Kamar yadda mazauna yankin suka shaida, jami’an soji da ’yan sa-kai sun bi sawun maharan daga baya suka kuma yi musayar wuta da su, lamarin da ya kai ga kubutar da wasu daga cikin fasinjojin da aka sace.

Kakakin ’yan sandan jihar, CSP William Aya, ya ce mutum biyu aka sace yayin da wani Raji Adesukami ya tsere, kuma an tura tawaga ta musamman domin ceto sauran.

Wata majiya ta rundunar soji ta bayyana cewa sojojin Birget ta 12 sun ceto mutane biyar a yayin wani samame da suka kai a yankin Isanlu–Egbe a ranar 29 ga Nuwamba, bayan wasu hare-haren sace mutane da suka afku a yankin.

A halin yanzu, Gwamna Usman Ododo ya ce za a kai farmaki kai tsaye cikin dazukan da ’yan bindiga ke ɓoyewa domin kare rayukan jama’ar jihar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Jam’iyyar PDP ta bukaci Tinubu ya janye jerin sunayen da ya tura majalisa domin tantancewa a matsayin jakadu

0

Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya janye jerin sunayen jakadu 32 da ya tura majalisar dattawa, tana mai cewa jerin ya ƙunshi mutane da ake kallon su marasa nagarta a idon ’yan Nijeriya da ma duniya. PDP ta ce wannan abu abin kunya ne ga diflomasiyyar ƙasar.

A cewar mai magana da yawun jam’iyyar, Comrade Ini Ememobong, PDP ta ce akwai sunayen mutane da ake zargi da aikata abubuwan da suka saba wa dimokuraɗiyya, ciki har da tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa saka shi a cikin jerin zai iya zama hanyar matsa wa sabon shugaban INEC wajen gudanar da zaɓe cike da kura-kurai kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

PDP ta ce tana bukatar a sake tura sunayen ’yan Nijeriya masu nagarta da tarihin kare dimokuraɗiyya, waɗanda za su wakilci ƙasar da mutunci a kasashen waje.

Jam’iyyar ta ce jinkirin da Shugaba Tinubu ya yi kafin fitar da jerin na nuna ƙarancin mutanen kirki da yake da su a kusa da shi.

Shugaba Tinubu ya sake miƙa sunayen sabbin Jakadu 32 ga majalisa domin tabbatarwa

0

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake aika sunayen mutane 32 ga Majalisar Dattawa don tantancewa a matsayin sabbin jakadu, kwanaki kaɗan bayan turo rukuni na farko na mutane uku.

A cewar wasikun da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, an nemi a gaggauta tantance jakadu 32, inda mata goma ke cikin jerin sunayen.

Daga cikin sunayen sun haɗa da Barr. Ogbonnaya Kalu, Reno Omokri, tsohon shugaban INEC Prof. Mahmud Yakubu, Erelu Angela Adebayo, da tsohon gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, tare da wasu shugabanni daga jihohi daban-daban ciki har da Tasiu Maigari, Prof. Nora Daduut, Femi Pedro, Femi Fani-Kayode, Fatima Ajimobi, Lola Akande da Victor Ikpeazu.

Hakazalika akwai Enebechi Okwuchukwu (Abia), Yakubu Danladi (Taraba), Miamuna Besto (Adamawa), Musa Abubakar (Kebbi), Syndoph Endoni (Bayelsa), Chima David (Ebonyi), Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun), da wasu jakadu daga jihohi daban-daban.

Ana sa ran za a tura sabbin jakadun zuwa ƙasashe masu muhimmancin hulɗa da Nijeriya kamar China, India, Canada, Mexico, UAE, Qatar, South Africa da Kenya, da cibiyoyi irin su Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO da Tarayyar Afirka, bayan tantancewarsu.

A makon da ya wuce Tinubu ya aika sunayen mutum uku na farko don a tura su zuwa UK, Amurka ko Faransa, inda ya tabbatar da cewa za a fitar da ƙarin sunayen jakadu nan gaba.

Akwai yiwuwar hambararren shugaban kasar Guinea Bissau ya kitsa juyin mulkin da aka yi masa gudun faduwa zabe – Jonathan

0

Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan, ya ce abin da ya faru a Guinea-Bissau ba juyin mulki na gaske ba ne, illa dabara da Shugaba Umaro Embaló ya kitsa don kauce wa fitar da sakamakon zabe.

Jonathan, wanda ya je kasar a matsayin mai sa ido kan zabe, ya dawo bayan rikicin ya barke ya ce abin mamaki ne ganin Embaló shi ne ya fara sanar da cewa an yi juyin mulki, sannan yana magana da kafafen yada labarai cikin ‘yanci, alamar cewa lamarin ba gaskiya ba ne. Ya ce hakan ya fi masa ciwo fiye da lokacin da ya fadi zaben 2015.

Juyin mulkin ya faru ne kwana guda kafin a bayyana wanda ya lashe zaben da Embaló da Fernando Dias suka kara. Daga baya, Kwamandan sojojin kasa, Horta Inta-A wanda ake alakanta shi da Embaló ya kama mulki, yayin da Embaló ya gudu zuwa Senegal.

Ganganci da gazawa suka sa gwamnatin Kano ke kira a kama ni – Ganduje

0

Tsohon Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya maida martani kan kiran da gwamnatin Kano ta yi na a kama shi, yana cewa wannan zargi na kafa wata rundunar ba shi da tushe balle makama.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Edwin Olofu, ya fitar, Ganduje ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta nuna gazawa ta hanyar karkatar da hankali daga matsanancin matsalar tsaron da ke addabar jihar.

Sanarwar ta zargi Gwamna Abba da kasa zuwa ko nuna tausayawa ga al’ummomin da ke fama da hare-hare, musamman mazauna Bagwai, Shanono, Tsanyawa da sauran wurare da ke cikin fargaba. Ganduje ya ce maimakon daukar matakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, gwamnatin ta dauki hanyar jifa da zargi marasa tushe.

Hakazalika, sanarwar ta kuma bayyana cewa Ganduje ba ya da alaka da tashin hankali wata dabi’a da ke barazana ga zaman lafiyar Kano, sannan ta jaddada cewa a tsawon mulkinsa na shekaru takwas jihar ta zauna cikin kwanciyar hankali.

Ganduje ya bukaci Gwamna Abba da ya maida hankali kan aiki da kundin tsarin mulki ya dora masa na kare mutanen Kano, maimakon yin abin da ya kira “wasan siyasa da wallafa zarge-zarge marasa amfani” don kau da hankali daga gazawar gwamnati.

Sheikh Dahiru Bauchi ya taimaki alhazan Nijeriya- Shugaban hukumar NAHCON

0

Shugaban hukumar aikin hajji ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar fitaccen malamin addini, Sheikh Dahiru Usman Bauchi inda ya ce marigayin ya kasance ginshiƙi wajen kula da jin daɗin alhazai da kuma gyaran tsarin aikin Hajji a Nijeriya.

A cikin sanarwar da aka fitar a Abuja ta hannun mai taimaka masa kan harkokin sadarwa, Ahmad Muazu, shugaban NAHCON ya miƙa ta’aziyya ga iyalai, almajirai da dukkan mabiyan marigayin, yana mai cewa wannan rashi babban gibi ne ga al’ummar Musulmi.

Usman ya bayyana cewa shawarwarin Sheikh Dahiru Bauchi sun taimaka wajen inganta tarbiyya da shirya ruhin masu zuwa aikin hajji, musamman idan an buƙaci jagora a lamurra masu sarkakiya da kuma hikimarsa ta kawo mafita da ta inganta tsarin hidima ga alhazai a yau.

Mutane 3 sun rasa rayukansu a wata gobarar tankar man fetur a jihar Kano

0

Mutane uku sun rasa rayukansu yayin da wani ya tsira da raunuka a wata gobara mabambanta da aka samu a jihar Kano a ranar Juma’a, kamar yadda hukumar kiyayewa da kashe gobara ta Jihar Kano ta sanar.

Gobarar ta farko ta faru ne da rana, kimanin karfe 1 na rana, lokacin da tankar mai mai dauke da lita 30,000 ta fadi a wajajen kasuwar Kura da ke hanyar Zaria.

A cewar hukumar, masu kashe gobara sun isa wurin nan da nan bayan samun kiran agaji daga tsohon jami’in Civil Defence, Danlami Muhammad. An samu mutane hudu da abin ya shafa; uku daga cikinsu sun mutu, yayin da mai napep ya tsira da rai.

Hukumar ta ce masu kashe gobara tare da jami’an ‘yan sanda da na kiyaye hadurra sun dakile wutar sannan suka mika gawarwakin ga ASP Ahmad Lawan na rukunin ‘yan Sanda na Kura. An tura motoci biyu na kashe gobara daga hedkwata da kuma ofishin Kura domin dakile gobarar.

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta yi ma manyan jami’anta karin karin girma

0

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar da kara girma ga jami’ai 28 daga Birgediya Janar zuwa Manjo Janar, tare da karin 77 daga Kanal zuwa Birgediya Janar. Wannan na zuwa ne a wani sabon tsarin sauya manyan shugabanni da rundunar ta sanar a shafinta na X ta bakin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a, Laftanar Kanal Appolonia Anele.

A jerin sabbin manyan janarori akwai O. Adegbe na Defence Intelligence Agency, S. M. Uba na Defence Information, R. E. Hedima na Military Intelligence, da R. T. Utsaha na Defence Operations.

Haka kuma, jaridar Punch ta ruwaito A. M. Umar na Warrant Officer Academy, S. Sulaiman daga Military Secretary, I. O. Bassey na Operations Centre, da C. A. Ekeator daga Makarantar kayan lantarki da injiniyoyi ta sojoji.

Rundunar ta kuma tabbatar da karin girma ga S. Y. Yakasai na Procurement, W. L. Nzidee daga sufuri, S. A. Emmanuel na Signals, S. S. Tilawan na Operation HADIN KAI, M. O. Agi na NDA, da I. M. Abbas, kwamandan Brigade 34. Jami’i Z. A. Saidu kuwa an ɗaga masa matsayi bayan rasuwarsa, a matsayin girmamawa ga hidimarsa.