DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 91

Rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta yi ma manyan jami’anta karin karin girma

0

Rundunar sojojin Nijeriya ta tabbatar da kara girma ga jami’ai 28 daga Birgediya Janar zuwa Manjo Janar, tare da karin 77 daga Kanal zuwa Birgediya Janar. Wannan na zuwa ne a wani sabon tsarin sauya manyan shugabanni da rundunar ta sanar a shafinta na X ta bakin mataimakin daraktan hulɗa da jama’a, Laftanar Kanal Appolonia Anele.

A jerin sabbin manyan janarori akwai O. Adegbe na Defence Intelligence Agency, S. M. Uba na Defence Information, R. E. Hedima na Military Intelligence, da R. T. Utsaha na Defence Operations.

Haka kuma, jaridar Punch ta ruwaito A. M. Umar na Warrant Officer Academy, S. Sulaiman daga Military Secretary, I. O. Bassey na Operations Centre, da C. A. Ekeator daga Makarantar kayan lantarki da injiniyoyi ta sojoji.

Rundunar ta kuma tabbatar da karin girma ga S. Y. Yakasai na Procurement, W. L. Nzidee daga sufuri, S. A. Emmanuel na Signals, S. S. Tilawan na Operation HADIN KAI, M. O. Agi na NDA, da I. M. Abbas, kwamandan Brigade 34. Jami’i Z. A. Saidu kuwa an ɗaga masa matsayi bayan rasuwarsa, a matsayin girmamawa ga hidimarsa.

Hedikwatar tsaron Nijeriya ta gayyaci sojojin da ake zargi da sakaci wajen sace daliban jihar Kebbi don ci gaba da bincikensu

0

Hedkwatar tsaron Nijeriya ta gayyaci dukkan sojojin da aka janye daga Government Girls’ Comprehensive SSS, Maga, a Danko/Wasagu, Jihar Kebbi, kafin sace dalibai 26 da ‘yan ta’adda suka yi domin ci-gaba da bincike.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hedikwatar tsaro ta kaddamar da bincike kan dalilin janyewar sojojin da gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sun kutsa makarantar ne ranar 17 ga watan Nuwamba, inda suka kashe mataimakin shugaban makarantar, Malam Hassan Makuku, sannan suka yi awon gaba da dalibai 26, daga ciki biyu sun tsere, ragowar 24 kuma suna hannun masu garkuwa har sai da gwamnatin tarayya ta sulhunta aka sako su.

Gwamna Nasir Idris ya bukaci a binciki dalilin janyewar sojojin duk da cewa jihar ta samu bayanan leken asiri da suka nuna cewa makarantar na cikin hadari.

Hakazalika, hakimin Maga, Muhammad Dantani, ya tabbatar da cewa sojojin sun bar wajen kimanin ƙarfe 1 na dare, kafin harin ya fara karfe 1:30 zuwa 3:30 na safe ba tare da turjiya ba.

Juyin mulkin Guinea Bissau ya fi mini ciwo fiye da shan kaye a zaben 2015 – Jonathan

0

Tsohon Shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa juyin mulkin da ya faru a Guinea Bissau ya fi masa ciwo fiye da lokacin da ya kira Muhammadu Buhari ya taya shi murna a zaben 2015 da ya sha kaye.

A cewarsa, lamarin ya taba shi sosai domin ya dade yana taka rawa wajen dawo da dimokuradiyya a kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A lokacin rikicin, Jonathan ya je Guinea Bissau ne a matsayin wakilin kungiyar dattawan Yammacin Afrika don sa ido kan zaben kasar, tare da tawagogin AU da ECOWAS. Sai dai kafin su kammala aikinsu, rundunar soji ta kwace mulki, lamarin da ya bar shi da tawagarsa cikin fargaba har aka kwashe su aka dawo da su Nijeriya ranar Alhamis.

Jonathan ya ce abin ya daga masa hankali sosai saboda bai taba tunanin zai tsinci kansa a irin wannan yanayi ba.

Hakazalika ya kara da cewa, abin da ya faru a Guinea Bissau ya fi masa ciwo fiye da ranar da ya kira Buhari bayan ya sha kaye a zabe, domin shi mutum ne da yake da yakinin dimokuradiyya.

Sanata Barau ya yi martani ga gwamnatin Kano bayan ta zarge shi da Ganduje da yunkurin kawo cikas ga tsaro

0

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya shawarci gwamnatin Kano ta daina sanya siyasa a cikin batun tsaron jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wasu kalamai da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Barau suka yi a kwanan nan, suna da hatsarin iya kawo cikas ga kokarin tabbatar da tsaro da gwamnatin jiha da ta tarayya ke yi a yanzu.

Sai dai a cikin sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya bayyana zargin gwamnatin jihar a matsayin maras tushe, yana mai kalubalantar gwamnatin ta fitar da bidiyon da ke nuna ya yi maganar da za ta iya ta’azzara matsalar tsaro.

Ƴan Nijeriya na da ƴancin neman taimakon ƙasashen waje kan matsalar tsaro idan gwamnati ta kasa – Obasanjo

0

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya ce ’yan Nijeriya na da cikakken ’yancin neman taimakon kasashen waje idan gwamnatin Nijeriya ta gaza kare rayukansu.

Obasanjo ya yi jawabin ne yayin wani taron Kirsimeti a Jos, inda ya ce bai kamata a ji kunyar neman taimako ba idan gwamnati ta kasa cika babban nauyinta na tsaro.

channels TV ta ruwaito Obasanjo ya ce a zamanin da ake amfani da tauraron dan adam da jiragen sintiri, bai kamata ’yan ta’adda su rika kashe mutane su bace ba. Ya zargi gwamnati da gazawa, yana mai cewa hare-hare da kashe-kashe sun yi yawa, kuma ’yan kasa sun gaji da zubar da jini.

Hakazalika, ya tuna da sace ’yan matan Chibok, yana mai cewa matsalar tsaro ta kara tabarbarewa maimakon ta inganta, kuma ya jaddada cewa kariyar ’yan kasa ita ce aikin farko na kowace gwamnati, amma a halin yanzu gwamnati ba ta iya kare al’umma yadda ya kamata ba.

Obasanjo ya kuma yi Allah-wadai da masu kokarin mayar da kashe-kashe batun addini ko kabila, yana mai cewa “dukkanmu ’yan Nijeriya ne, kuma ana kashe mu ba tare da bambanci ba.”

Sojojin Nijeriya sun kama wadanda ake zargi da satar mutane 56 tare da ceto 45 cikin mako ɗaya

0

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun halaka ’yan ta’adda da dama, sun kama mutane 57 da ake zargi, tare da ceto mutane 45 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda, a cewar daraktan yaɗa labaran tsaro, Manjo-Janar Michael Onoja.

A cewarsa, dakarun sun kuma kwato makamai, motoci da harsasai, tare da rusa sansanonin ’yan ta’adda a yankuna daban-daban kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai ta kashe ’yan ta’adda da dama, ta kama mutane 11 da ake zargi da taimaka musu, ta kuma kubutar da fasinjoji 8 da aka sace. Jiragen yakin sama sun yi luguden wuta a dajin Sambisa, inda suka halaka ’yan ta’adda tare da lalata wuraren boye makamansu.

Haka kuma, dakarun Operation FASAN YAMMA, sun hallaka ’yan bindiga da dama, tare da kama 15, da kuma ceto mutane 13 a jihohin Zamfara, Kebbi, Sokoto, Katsina, Kaduna da Neja. Dakarun sun kuma kwato makamai, motocci, dabbobi da kuma wani dillalin makamai dauke da Naira miliyan 4 da makamai irin na soji.

Gwamnonin Arewacin Nijeriya sun karbi Naira biliyan 56 a cikin wata 9 don inganta tsaro

0

Wani bincike da jaridar Punch ta ruwaito ya nuna jihohi 14 na Arewacin Nijeriya sun karbi Naira Biliyan 56 domin inganta tsaro a cikin watanni tara na 2025, duk da cewa hare-haren ’yan bindiga da garkuwa da mutane sun ƙara tsananta a jihohin Neja, Kebbi, Kano da Kwara.

Daga cikin manya-manyan hare-haren akwai sace dalibai 315 da malamai 13 a Papiri, tare da ƙarin mutane 26 a Kebbi da 24 a Shiroro.

Yawaitar hare-haren ya tayar da hankulan jama’a, musamman bayan an sake yin garkuwa da mata masu juna biyu, yara da masu shayarwa a Kwara da Kano cikin mako guda. Lamarin da ya tilasta shugaba Tinubu ayyana dokar gaggawa kan tsaro tare da umartar daukar karin jami’an tsaro 20,000.

Duk da cewa kuɗin inganta tsaro na nufin daukar matakan gaggawa da tattara bayanan sirri, jama’a na zargin ana batar da kudaden ne kawai ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba.

Binciken ya nuna jihohin sun kashe kusan rabin Naira Biliyan 101 da suka ware a 2025, amma hare-hare na ci-gaba da yi wa Arewa barazana.

Wike ya soke lasisin iznin mallakar filayen Ganduje, Sule Lamido, Patience Jonathan, Iyabo Obasanjo da karin wasu mutane

Fitattun sunayen da jaridar PREMIUM TIMES ta gani a jerin waɗanda Ministan na Abuja Nyesom Wike ya soke lasiain mallakar filayen na su, sun haɗa da Uwargidan tsohon Shugaban Nijeriya, Patience Jonathan, tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma, tsohon babban Sojojin Ƙasa na Nijeriya, Ishaya Bamaiyi, da Iyabo Obasanjo, ‘yar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Sauran sunayen sun haɗa da; Sarkin Ilorin Ibrahim Sulu-Gambari; tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Uche Secondus, da tsohon mukaddashin shugaban jam’iyyar, Abubakar Baraje.

Tsofaffin gwamnoni da aka soke musu takardun mallakar ƙasa sun haɗa da Abdullahi Ganduje (Kano), Sule Lamido (Jigawa), Ayo Fayose (Ekiti), Olagunsoye Oyinlola (Osun), Donald Duke (Cross River), Niyi Adebayo (Ekiti), Ibrahim Dankwambo (Gombe) da Aliyu Wamakko (Sokoto).
Tsofaffin ministocin da ke cikin jerin sun haɗa da Kema Chikwe, Dapo Sarumi, Idika Kalu, Olu Agunloye, da Inna Ciroma.

‘Yan majalisa masu ci da wadanda suka taba zama ‘yan majalisa da sunayensu ke cikin jerin sun haɗa da Ali Ndume (Borno), Osita Izunaso (Imo), Caleb Zagi (Kaduna), Ganiyu Solomon (Lagos), Olabode Olajumoke (Ondo), Iya Abubakar (Adamawa), Abubakar Sodangi (Nasarawa), Iyiola Omisore (Osun), Patrick Obahiagbon (Edo), Usman Bugaje (Katsina), Abba Aji (Borno), Shehu Agaie (Niger), Patience Ogodo (Ebonyi), da Mao Ohuabunwa (Abia), wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na ɓangaren PDP na Wike.

Fitattun ‘yan Nijeriya da suka rasu amma sunayensu ke cikin jerin sun haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na NRC a 1993, Bashir Tofa, tsohon shugaban BoT na PDP kuma minista, Tony Anenih, tsohon Ministan Kuɗi, Adamu Ciroma; tsohon jagoran Ohanaeze, Emmanuel Iwuanyanwu; wani tsohon shugaban Ohanaeze, Ralph Uwechue; tsoffin ministoci Alex Akinyele, Dubem Onyia, Onaolapo Soleye, Yakubu Lame, Babatunde Osotimehin, da John Odey.

Tsohon gwamnan Anambra Chinwoke Mbadinuju, tsohon IGP Ibrahim Coomassie, da Sanatan Delta North Patrick Osakwe, su ma sun rasu amma sunayensu na cikin jerin.

Hukumomin gwamnatin tarayya da lamarin ya shafa sun haɗa da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), NNPCL, ma’aikatun tarayya na Kuɗi, Muhalli, CBN, NTA, NPA, FHA, RMFAC, NAN; Rundunar Sojan Ruwa da Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya.

Al’amura sun fara komawa daidai a Guinea Bissau

0

Al’amura sun fara komawa daidai a Guinea Bissau bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sojoji sun nada Janar Horta N’Tam, a matsayin shugaban na rikon kwarya na tsawon shekara guda bayan kifar da gwamnati a ranar Laraba.

Rahoton ya ce juyin mulkin ya faru ne kwana guda kafin a bayyana sakamakon zaben 23 ga Nuwamba.

A safiyar Juma’a, motocin haya a manyan tituna sun dawo zirga-zirga, shaguna da kasuwanni sun fara budewa, duk da cewa har yanzu an tsaurara tsaro a wasu muhimman wurare.

Trump zai haramta wa ‘yan Nijeriya komawa Amurka da zama

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sabon tsari da yake neman dakatar da shigar mutane Amurka daga kasashe daban-daban ciki har da Nijeriya.

Trump ya sanar da hakan ne yayin yayin wani biki inda ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu ya janyo tabarbarewar tsaro da matsin lamba ga hidimomin gwamnati.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito Trump na cewa, yawan ’yan kasashen waje da ke zaune a Amurka ya kai mutum miliyan 53, abin da ya ce ya taimaka wajen yawaitar laifuka, cunkoso a asibitoci da kuma tashe-tashen hankula.

Shugaban ya yi zargin cewa shigowar ’yan gudun hijira daga Somalia zuwa Minnesota, ya sauya yanayin al’ummar jihar ta hanyar da ya ce ba ta da kyau.