DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 92

Al’amura sun fara komawa daidai a Guinea Bissau

0

Al’amura sun fara komawa daidai a Guinea Bissau bayan juyin mulkin da aka yi a kasar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa sojoji sun nada Janar Horta N’Tam, a matsayin shugaban na rikon kwarya na tsawon shekara guda bayan kifar da gwamnati a ranar Laraba.

Rahoton ya ce juyin mulkin ya faru ne kwana guda kafin a bayyana sakamakon zaben 23 ga Nuwamba.

A safiyar Juma’a, motocin haya a manyan tituna sun dawo zirga-zirga, shaguna da kasuwanni sun fara budewa, duk da cewa har yanzu an tsaurara tsaro a wasu muhimman wurare.

Trump zai haramta wa ‘yan Nijeriya komawa Amurka da zama

0

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sabon tsari da yake neman dakatar da shigar mutane Amurka daga kasashe daban-daban ciki har da Nijeriya.

Trump ya sanar da hakan ne yayin yayin wani biki inda ya ce tsarin da ake amfani da shi yanzu ya janyo tabarbarewar tsaro da matsin lamba ga hidimomin gwamnati.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito Trump na cewa, yawan ’yan kasashen waje da ke zaune a Amurka ya kai mutum miliyan 53, abin da ya ce ya taimaka wajen yawaitar laifuka, cunkoso a asibitoci da kuma tashe-tashen hankula.

Shugaban ya yi zargin cewa shigowar ’yan gudun hijira daga Somalia zuwa Minnesota, ya sauya yanayin al’ummar jihar ta hanyar da ya ce ba ta da kyau.

An sace mutane a karamar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi, kwanaki kadan bayan an ceto dalibai ‘yan mata na makarantar Maga

0

Kwana guda bayan ceto ɗalibai mata 24 daga hannun ’yan bindiga, an sake samun rahoton sace mutane da dama a ƙauyen Kurmaci da ke Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu a Jihar Kebbi.

’Yan bindigar, kimanin su fiye da 30, sun kai farmaki a daren Laraba lokacin da mazauna yankin ke barci.

A yayin harin, an sace mutanen da ba a tantance adadinsu ba, yayin da wasu da dama suka jikkata.

Wani mazaunin yankin Aliyu Dangaladima ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa, wannan hari shi ne na uku da ƙauyen ya fuskanta cikin wata guda.

Hukumar EFCC ta gayyaci Abubakar Malami

Tsohon Babban Lauyan Gwamnatin Nijeriya, Abubakar Malami ya bayyana cewa zai halarci gayyatar da Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta yi masa domin yin bayani kan wasu al’amura da ake bincike a kansu.

Malami, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce a matsayinsa na ɗan ƙasa mai bin doka da oda, ya dauki matakin amsa wannan kira ba tare da wani jinkiri ko tangarda ba.

Ya ce ya dade yana tsayawa kan gaskiya da riƙon amana a aikinsa na hidimar jama’a, tare da tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa zai rika sanar da su duk wani ci gaban da zai biyo bayan wannan lamari.

Goodluck Jonathan ya baro Guinea-Bissau cikin koshin lafiya – Gwamnatin Nijeriya

0

Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Ebele Jonathan, yana cikin koshin lafiya kuma ya bar Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin kasar, in ji sanarwar gwamnatin Nijeriya a ranar Alhamis.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje Nijeriya, Kimiebi Ebienfa ne ya tabbatar da hakan yayin da yake tattaunawa da manema labarai a Abuja, inda ya ce Jonathan ya tashi tare da tawagarsa ciki har da Mohamed Chambas.

Ma’aikatar ta ce Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban kwamitin kula da zabe na zauren dattawan yammacin Afirka, domin sa ido kan zaben shugaban kasa da na majalisa da aka gudanar a ranar Lahadi, kafin sojoji su sanar da cewa sun karɓe mulki.

Bayan rufe iyakokin kasar, a ranar Alhamis hukumomin sojin suka sanar da bude iyakokin, inda Janar Lansana Mansali, babban mai kula da rundunar

sojin Guinea-Bissau, ya tabbatar da daukar matakin.

Sojoji a Guinea-Bissau sun rantsar da sabon shugaban rikon kwarya

0

A ranar Alhamis, rundunar sojin Guinea-Bissau ta sanar da cewa an rantsar da Janar Horta Nta Na Man a matsayin sabon shugaban rikon kwarya, kwana guda bayan da suka hambarar da gwamnatin kasar.

A cewar sanarwar da sojin ƙasar suka fitar, rantsuwar ta biyo bayan jawabin da hafsoshin rundunar suka yi tun a ranar Laraba inda suka bayyana cewa sun kifar da shugaban ƙasar da ke kan mulki.

Rahotanni daga France24 sun bayyana cewa wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara samun tashe-tashen hankula a yankin Yammacin Afirka, musamman game da karuwar juyin mulki a wasu kasashe.

Majalisar wakilan Nijeriya ta nemi a ceto Jonathan daga Guinea-Bissau

0

Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta amfani da dukkan matakan diflomasiyya domin ganin ta dawo da tsohon shugaba Goodluck Jonathan cikin koshin lafiya daga Guinea-Bissau, inda yake makale sakamakon juyin mulkin da aka yi a ranar Laraba.

Dan majalisa Julius Ihonvbere ne ya gabatar a yayin zaman majalisar wakilan na ranar Alhamis.

A cewar Ihonvbere, Jonathan ya je Guinea-Bissau ne domin sa ido kan zaben kasar, amma ya makale lokacin da sojoji suka karbe mulki bayan lokacin sanar da sakamakon zabe ya kusa. Majalisar ta bukaci gwamnati ta yi duk mai yiwuwa domin ganin dawowarsa lafiya.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa dubban masu sa ido kan zabe daga kasashe daban-daban sun makale a filin jirgi tun ranar Laraba, bayan sojoji sun karbe ikon kasar tare da saka dokar hana fita a kasar.

Ghana ta nemi a mayar da mulkin dimukuradiyya a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin soji

0

Gwamnatin Ghana ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai bayyana shi a matsayin karɓar mulki ta hanyar saba wa doka da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ranar 26 ga Nuwamban 2025, hukumomin Ghana sun ce juyin mulkin ya lalata tsarin siyasa bayan kammala zaben shugaban ƙasa da na majalisar dokoki da aka yi ranar 23 ga Nuwamba.

Rahotanni sun ce wannan juyin mulki ya dakile sanar da sakamakon zaben da aka shirya fitarwa ranar 27 ga Nuwamba.

Ghana ta nuna tsananin damuwa da bacin rai, tana mai kiran abin a matsayin yunƙurin take muradun jama’ar Guinea-Bissau, inda ta nemi a gaggauta dawo da mulkin dimukradiyya, tare da kira ga duk bangarorin ƙasar su mutunta tsarin dimokuraɗiyyar.

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin Guinea-Bissau

0

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya da zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje Kimiebi Ebienfa ya fitar a Alhamis din nan, gwamnatin ta ce ta samu labarin juyin mulkin kuma hakan na da matuƙar takaici da damuwa.

Sanarwar ta ce Nijeriya ba ta amince da wannan abu da ke ruguza da tsarin mulki da ci gaban dimokuraɗiyya ba, kuma ba iya a Guinea-Bissau kawai ba, har ma a yankin ECOWAS gaba ɗaya.

Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan mataki ya karya ka’idar ECOWAS wanda ta yi kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki, tare da haramta karɓar mulki ta hanyar da ba ta dace ba.

Janye ‘yansanda daga tsaron manyan mutane zai jefa mu cikin haɗari – Sanatoci

0

Sanatoci da dama sun nuna damuwa kan umarnin Shugaba Tinubu na janye jami’an ’yan sanda daga tsaron manyan mutane, suna cewa matakin na iya barin su cikin barazanar tsaro.

Sanatocin sun bayyana wannan damuwar ne a zaman majalisar ranar Laraba yayin tattaunawa kan tabarbarewar tsaro, bayan gabatar da kudiri daga Sanata Oyelola Yisa Ashiru kan bukatar gaggawar duba lamarin daga gwamnatin tarayya.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a janye jami’an daga tsaron manyan mutane domin mayar da su kan ayyukan su na asali, lamarin da ya janyo cece-kuce a majalisar dattawa da ta wakilai.

A lokacin muhawarar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce wannan mataki bai dace ba a lokacin da hare-haren ’yan bindiga ke karuwa, yana mai cewa jami’an gwamnati na daga cikin manyan da ke bukatar tsaro.

Shi ma Sanata Tahir Monguno daga Borno ya ce janye ‘yansandan daga jami’an gwamnati zai kara mayar da su abin hari, ganin yadda yanayin tsaro ke tabarbarewa a sassan kasar.