DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 93

Ghana ta nemi a mayar da mulkin dimukuradiyya a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin soji

0

Gwamnatin Ghana ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai bayyana shi a matsayin karɓar mulki ta hanyar saba wa doka da kuma barazana ga dimokuraɗiyya a Yammacin Afirka.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ranar 26 ga Nuwamban 2025, hukumomin Ghana sun ce juyin mulkin ya lalata tsarin siyasa bayan kammala zaben shugaban ƙasa da na majalisar dokoki da aka yi ranar 23 ga Nuwamba.

Rahotanni sun ce wannan juyin mulki ya dakile sanar da sakamakon zaben da aka shirya fitarwa ranar 27 ga Nuwamba.

Ghana ta nuna tsananin damuwa da bacin rai, tana mai kiran abin a matsayin yunƙurin take muradun jama’ar Guinea-Bissau, inda ta nemi a gaggauta dawo da mulkin dimukradiyya, tare da kira ga duk bangarorin ƙasar su mutunta tsarin dimokuraɗiyyar.

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin Guinea-Bissau

0

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah-wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau, tana mai cewa hakan barazana ce ga dimokuraɗiyya da zaman lafiyar yankin Yammacin Afirka.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje Kimiebi Ebienfa ya fitar a Alhamis din nan, gwamnatin ta ce ta samu labarin juyin mulkin kuma hakan na da matuƙar takaici da damuwa.

Sanarwar ta ce Nijeriya ba ta amince da wannan abu da ke ruguza da tsarin mulki da ci gaban dimokuraɗiyya ba, kuma ba iya a Guinea-Bissau kawai ba, har ma a yankin ECOWAS gaba ɗaya.

Gwamnatin ta ƙara da cewa wannan mataki ya karya ka’idar ECOWAS wanda ta yi kan dimokuraɗiyya da kyakkyawan mulki, tare da haramta karɓar mulki ta hanyar da ba ta dace ba.

Janye ‘yansanda daga tsaron manyan mutane zai jefa mu cikin haɗari – Sanatoci

0

Sanatoci da dama sun nuna damuwa kan umarnin Shugaba Tinubu na janye jami’an ’yan sanda daga tsaron manyan mutane, suna cewa matakin na iya barin su cikin barazanar tsaro.

Sanatocin sun bayyana wannan damuwar ne a zaman majalisar ranar Laraba yayin tattaunawa kan tabarbarewar tsaro, bayan gabatar da kudiri daga Sanata Oyelola Yisa Ashiru kan bukatar gaggawar duba lamarin daga gwamnatin tarayya.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a janye jami’an daga tsaron manyan mutane domin mayar da su kan ayyukan su na asali, lamarin da ya janyo cece-kuce a majalisar dattawa da ta wakilai.

A lokacin muhawarar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce wannan mataki bai dace ba a lokacin da hare-haren ’yan bindiga ke karuwa, yana mai cewa jami’an gwamnati na daga cikin manyan da ke bukatar tsaro.

Shi ma Sanata Tahir Monguno daga Borno ya ce janye ‘yansandan daga jami’an gwamnati zai kara mayar da su abin hari, ganin yadda yanayin tsaro ke tabarbarewa a sassan kasar.

APC ta haramta tallata duk wani mai neman takara a jihar Katsina

0

Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta yi gargaɗi tare da haramta tallata duk wani mai neman takara ko ɗaga allon hotunan su a lokacin zagayen da Gwamna Radda zai yi na ƙananan hukumomin jihar.

Shugaban jam’iyyar na jihar Katsina Sani JB Daura ta fitar da wannan sanarwa bayan kammala zama da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Katsina.

Alhaji Sani JB ya ce yanzu ba lokacin siyasa ba ne da za a rika daga allunan talla da hotunan masu neman takara. Ya kara da yin kira ga dukkan wasu masu mukaman gwamnati ko masu neman takara da su kiyaye wannan doka.

Ya ce Gwamnan zai yi zagaye ne don duba irin ci gaba da aka samar da karin korafe-korafen jama’a domin a lalubo hanyoyin warware su.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da manoma 20 a jihar Neja

0

Akalla mutane 20 ne wadanda suka kunshi manoma, mata masu juna biyu da kuma yara ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Unguwan Kawo da ke yankin Erena da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.

Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4 na yammacin Laraba, 26 ga Nuwamba, a lokacin da manoman ke girbin shinkafa.

A cewar wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa yace dansa na ɗaya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, inda ya ce gonar da abin ya faru tana da tazarar kimanin mita 500 ne kacal da Erena, inda sansanin sojoji yake.

Lamarin ya faru ne kwanaki shida bayan sace dalibai da malamai sama da 200 daga makarantar St. Mary a Papiri, Karamar Hukumar Agwara.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya ce zai bincika tare da tabbatar da sahihan bayanai nan gaba kadan.

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu 

Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu kamar yadda daya daga cikin ‘ya’yansa ya tabbatar wa da DCL Hausa. Ya shaida mana cewa fitaccen malamin addinin ya rasu ne a safiyar Alhamis din nan a garin Bauchi

Allah ya albarkaci Sheikh Dahiru Bauchi da ‘ya’ya da dama. Khalid Abdullahi Zaria wanda ya rubuta littafi na musamman kan rayuwar malamin ya ce Sheikh Dahiru Bauchi na da ‘ya’ya 95, 48 daga cikinsu mata ne. A cikinsu guda 77 sun haddace Qur’ani.

An haifi fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ke jagorantar Darikar Tijjaniyya a Najeriya, da ake hasashen shekarunsa sun haura 100 kafin Allah Ya karbi rayuwarsa. Tuni wannan labari ya jefa gaba daya duniyar Musulunci a Nijeriya da suaran kasashen Afirka ta yammam musamman mabiyansa, almajiransa, da ‘yan uwa cikin jimami.

Tun yana karamin yaro ya fara karatun Alƙur’ani karkashin jagorancin mahaifinsa, Alhaji Usman Adam, har ya haddace Qur’ani Mai Tsarki kafin ya girma.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi karatu a wajen malamai irinsu Sheikh Usman Zangon Barebari, Sheikh Abdulkadir Zaria, da Sheikh Abubakar Atiku — sannan daga baya ya karbi Darikar Tijjaniyya tare da zurfafa iliminsa a fannin tafsiri, hadisi.

Sheikh Bauchi ya kwashe shekaru da dama yana gudanar da tafsirin Alƙur’ani — a zahiri tun wajen shekarun 1950, jim kadan bayan da ya yi auren fari a 1948.

Karfin iliminsa da tasirinsa a darikar Tijjaniya ya sa ya yi nasarar samar da mutane fiye da 140,000 da suka haddace Qur’ani a cibiyoyin da ya gina a Nijeriya da sauran kasashe, a cewar rahoton Daily Trust da aka wallafa a shekarar 2022.

Harbe-harbe ya sa an kulle wasu wurare a fadar White House ta Amurka

0

An kulle fadar White House, ta Amurka, tare da wasu muhimman gine-ginen gwamnati sakamakon harbin da aka yi kusa da fadar shugaban ƙasar.

An harbi sojoji biyu na National Guard a inda lamarin ya faru kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Gwamna Patrick Morrisey ya fara bayyana cewa an kashe dakarun, amma daga baya ya ce rahotannin da yake samu sun yi karo da juna game da halin da sojojin suke ciki, inda ya ƙara da cewa za a fitar da cikakken bayani idan an tabbatar.

Ya kamata Tinubu ya sake duba yuwuwar janye ‘yan sanda daga tsaron manyan mutane – Idris Wase

Tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilan Nijeriya Hon. Idris Wase, ya roƙi shugaba Tinubu da ya sake duba umarnin da ya bayar na janye ’yan sanda daga tsaron manyan mutane, domin ‘yan bindiga na yi musu barazana.

A lokacin da Majalisar ke tsaka da muhawara a Larabar nan Wase ya yi wannan bayani, yana mai jaddada cewa akwai bukatar shugaban ya fayyace rukunin manyan mutane da janyewar ta shafa.

Wannan korafin na zuwa ne bayan Tinubu ya bada umarni a Abuja ranar Lahadi, lokacin taron tsaro tare da hafsoshin tsaro da daraktan hukumar DSS.

Tinubu ya zabi jakadun Nijeriya a kasashen waje

0

Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane uku ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin jakadu na Nijeriya a wasu kasashen waje.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya bayyana cewa jerin sunayen farko ya kunshi mutum uku ne kawai.

A cewar Akpabio, sunayen da shugaban kasa ya aika sun hada da Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa sai Ayodele Oke daga jihar Oyo.

Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da gwamnati ke ci gaba da cike guraben diflomasiyya da suka yi saura tun bayan rushe sunayen wadancan jakadu a farkon mulkin Tinubu.

An sake yunkurin yin juyin mulki a Guinea-Bissau

0

Rahotanni sun yi nuni da cewa an sake yunkurin yin juyin mulki a kasar Guinea-Bissau.

 

Wannan ya zo ne bayan da shugaba mai ci Umaro Sissoco Embaló ya bayyana hasashen sa na samun nasara a zaben shugaban kasar da ya gudana a makon da ya gabata da kashi 65 na kuri’u.

 

’Yan jarida da ke ruwaito zabe sun bayyana cewa lamarin tsaro ya taɓarɓare a babban birni, inda aka jiyo karar harbe-harbe a kewayen ofishin hukumar zabe ta kasar (CNE).