DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 95

Abin kunya ne rufe makarantu a Arewa saboda matsalar tsaro – Buba Galadima

0

Jigo a jam’iyyar NNPP Buba Galadima, ya soki matakin wasu gwamnatocin Arewa na rufe makarantu saboda karuwar sace-sacen dalibai, yana bayyana matakin a matsayin abin kunya da rashin hangen nesa.

Buba Galadima ya furta haka ne a lokacin da yake hira a gidan talabijin na Arise a inda ya ce matsalar tsaro da ta kunno kai musamman a jihar Neja da sauran jihohi ba dalili ba ne da zai sa a tsaida karatu.

Ya jaddada cewa abin da ya kamata shi ne ƙarfafa tsaro a makarantun da ke fadin Arewa, tare da yin amfani da fasahohin zamani wajen gano barazana tun kafin ta faru.

A cewarsa yawancin hare-haren na faruwa ne saboda rashin amfani da bayanan sirri da ake samu da wuri.

Babban Sufetan ‘yan sandan Nijeriya ya kai ziyara jihar Kebbi

0

Wannan ziyara ta zo ne bayan labarin mummunar harin da ‘yan bindiga suka kai makarantar a ranar 17 ga Nuwamba.

A cewar jaridar Punch, Egbetokun zai gana da gwamnan jihar, Nasir Idris, sannan ya yi jawabi ga jami’an rundunar ‘yan sanda da ke jihar.

Ziyarar tasa ta taso ne bayan ya yi wa Shugaba Tinubu bayanin tsaro, inda aka tattauna karuwar hare-hare da sace mutane a jihohin Kebbi, Neja da Kwara.

Rahoton ya ce manyan hafsoshin tsaro sun halarci taron, ciki har da babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyode, da Air Vice Marshal Kelvin Aneke, da Rear Admiral Idi Abbas, da sauran shugabannin rundunonin tsaro.

Masu garkuwa da mutane sun nemi kudin fansa miliyan 10 kafin su sakesu

0

Wadanda sukai garkuwa da mata 13 da aka sace a jihar Borno sun nemi kudin fansa Naira miliyan 10 domin sakin su.

Jaridar Daily Trust, ta ruwaito cewa ‘yan ta’adda ne suka sace matan manoman a ranar Asabar.

Wani ɗan uwa ga ɗaya daga cikin wadanda aka sace ya bayyana cewa masu garkuwar sun kira ta ne bayan sun saki wata matashiya da ke shayarwa, ya ce an sake ta sannan aka kwace wayarta, aka ba ta sabon layin waya domin ta saka a gida sannan kuka kira suka bayyana bukatarsu.

Ya bayyana cewa al’ummar yankin ba su da karfin biyan wannan kudin, domin yawancinsu manoma ne kuma suna fama da rayuwa.

Harin kwanton-bauna ya yi sanadiyyar ajalin ‘yan sanda hudu a jihar Bauchi

0

An yi wa jami’an ‘yan sanda hudu da aka halaka a kwanakin baya a wani kwanton-bauna a Sabon Sara, Karamar Hukumar Darazo ta Jihar Bauchi, jana’iza a jiya.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa jami’an sun fada tarkon ‘yan bindiga ne yayin wani aiki da suke yi a karshen mako.

An gudanar da sallar jana’izar Musulman hudu a Babban Masallacin JIBWIS Gwallaga, tare da rakiyar iyalan mamatan da dubban al’umma zuwa makabartar Dungulbi, inda aka birne su bisa koyarwar addinin Musulunci.

A cikin wata sanarwa, da mai magana da yawun rundunar, SP Ahmed Wakil, ya fitar ya ce rundunar na cikin alhini, yana mai yabawa jarumtar jami’an, ya ce goyon bayan da suka ba al’umma da jajircewar da suka nuna wajen kare rayuka da dukiyoyi ba za a manta wa da shi ba.

Fashewar tankar man fetur ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dama a jihar Neja

0

Fashewar wata tankar man fetur a cikin gidan mai a Tungan Bunu, karamar hukumar Rijau da ke jihar Neja ta yi sanadiyyar lalata gidaje da dukiyoyi masu tarin yawa a daren Litinin.

Lamarin ya haifar da firgici a yankin, inda mutane suka yi ta gudun ceton rai.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa wata majiya ta shaida mata cewa tankar ta iso ne domin sauke mai sai kawai ta kama da wuta, wacce ta fantsama zuwa gidajen dake kusa da su.

Rahoton ya kara da cewa wata tanka ta daban dauke da man fetur ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya rufe hanyar gaba ɗaya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa tankar dai ta fito daga Legas zuwa Gombe ne, inda ta kife bayan tankin ya balle daga jikin kan motar.

Lokaci ya yi da za a kafa ‘yan sandan jihohi – gwamnonin Kudu Maso Yammacin Nijeriya

0

Gwamnonin yankin Kudu Maso Yamma sun sake jaddada bukatar kafa ‘yan sandan jihohi, suna cewa karuwar matsalolin tsaro a fadin Nijeriya ta kai matakin da ba za a yi gum ba.

Gwamnonin sun bayyyana haka ne bayan taron gaggawa da suka gudanar a Ibadan, jihar Oyo.

A cikin wata sanarwa da suka fitar, Gwammnonin karkashin jagorancin gwamnan Legasa Babajide Sanwo-Olu, dukkanninsu sun amince da matsayar da aka cimma.

A cewar sanarwar, gwamnonin sun bukaci Gwamnatin tarayya ta gaggauta shiga cikin batun tsare-tsaren dazuzzuka, wadanda suka ce sun zama maboyar miyagu, yayin da suka tabbatar da bukatar kafa ‘yan sandan jihohi abinda suka ce sune za su daukin nauyinsu, saboda za su taimaka wajen dakile matsalar tsaro da ake fama da ita.

Gwamnan Kebbi ya soki rundunar sojin Nijeriya kan yadda take yakar rashin tsaro

0

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ya nuna rashin gamsuwa da tsarin da rundunar soji ke amfani da shi wajen yakar rashin tsaro yana mai kira da a sauya dabarar aiki.

Gwamman ya bayyana haka ne a Litinin din nan lokacin da ya karɓi bakuncin ‘yan Majalisar wakilai karkashin jagorancin kakakin Majalisar Tajudeen Abbas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito gwamnan na sake jaddada bukatar yin bincike kan janye jami’an tsaro daga makarantar ta ‘yan mata ta Maga mintuna kaɗan kafin ’yan bindiga su sace ’yan mata 25.

A cewar gwamnan abin mamaki ne yadda ‘yan bindiga fiye da 500 ke yawo a babura a manyan hanyoyi ba tare da an dakatar da su ba, duk da cewa gwamnati na ba da tallafi, kayan aiki, da motoci ga jami’an tsaro.

Sace dalibai na barazana ga makomarsu a Arewacin Nijeriya – Amnesty International

0

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International a Nigeria ta yi gargadin cewa yawaitar sace dalibai a makarantun arewa na iya karya ilimi, tare da jefa rayuwar yara cikin mummunar makoma.

A wata hirar da ya yi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, daraktan Amnesty a Nijeriya Isa Sanusi ya ce tsananin tsoro da fargabar sace dalibai na hana su zuwa makaranta, lamarin da ke kara dagula fannin ilimi a yankin.

Sanusi ya bayyana cewa iyayen da ke fama da talauci musamman a karkara na fama wajen tura yaransu makaranta, a yayin da rashin tsaro da sace-sacen yara zai kara hana su yarda da aika ’ya’yansu makaranta.

Ya ce tsoron sace wa kaɗai zai hana dubban yara samun ilimi a arewacin Nijeriya wanda a yanzu yaran da ba sa zuwa makaranta sun haura miliyan 12.

Makarantun Sakandire na je-ka-ka dawo za su ci gaba da karatu – Gwamnatin Katsina

0

Gwamnatin jihar Katsina ta bai wa makarantun firamare da sakandare na je-ka-ka-dawo damar ci gaba da karatu

A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta jihar ta fitar, ta ce anyi haka ne domin ba da damar zana jarabawar zangon karatu na farko.

Sanarwar ta ce duk da haka dukkannin makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai bayan wani sabon umarni bisa matakan da Gwamnatin jihar Katsina ta dauka don ƙara tsaurara tsaro da kare rayukan ɗalibai da malamai a fadin jihar.

Ma’aikatar ta umurci shugabannin makarantun je-ka-ka dawo da sauran masu ruwa da tsaki su kiyaye tsari da bin dokoki tare da kira ga iyaye su ba ’ya’yansu cikakken goyon baya.

Gwamnatin jihar Bauchi ta rufe dukkanin makarantun da ke fadin jihar

0

Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da rufe dukkan makarantu firamare, sakandare da manyan makarantu ciki har da na masu zaman kansu sakamakon matsalar tsaro.

Rufe makarantun ya biyo bayan munanan hare-hare da aka kai kwanakin nan ciki har da sace dalibai a jihohin Neja da Kebbi.

Haka kuma ‘yan bindiga sun halaka ‘yan sanda biyar a kauyen Sabon Sara a ƙaramar hukumar Darazo ta jihar kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar Bauchin ta tabbatar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Ilimi ta jihar Bauchi Jalaludeen Usman ya fitar, gwamnati ta ce rufe makarantun ya biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro tare da la’akari da tsaron dalibai da malamai.