DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 96

Jam’iyyar PDP ta bukaci Shugaba Tinubu ya nemi taimako ko ya yi murabus

0

Jam’iyyar PDP ta na shawartar Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nemi taimako ko ya yi murabus, sakamakon yawaitar hare haren ‘yan bindiga da sace sacen ɗalibai da ya addabi jihohin Arewa a kwanakin nan.

A wani taron manema labarai da jam’iyyar ta yi a Abuja, mai magana da yawunta na ƙasa Ini Ememobong ya ce sace ɗalibai a jihar Kebbi da Niger da kuma masu ibada a Kwara na nuna gazawar Gwamnatin Tinubu wajen magance matsalar tsaro.

A cewar sa gwamnati ta gaza aikinta na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasa, yana mai jaddada cewa idan gwamnati ta kasa wannan aiki to ga dole ta nemi taimako daga cikin gida ko wajen ƙasa.

PDP ta ce matakin rufe wasu makarantun da wasu jihohi ke yi babu inda zai kai, domin hakan kamar mika wuya ne ga ‘yan ta’adda.

Atiku zai yi rijistar jam’iyyar ADC a Litinin din nan – Daily Trust

Tsohon dan takarar shugabancin Nijeriya Atiku Abubakar zai yi rajista a jam’iyyar ADC a Litinan din nan tare da magoya bayansa.

Wata majiya ta tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa an kammala dukkan shirye-shirye domin yin rajistar ta sa a unguwarsa ta Jada Ward 1, jihar Adamawa, sa’annan zai gana da shugabannin jam’iyyar a Yola.

A baya dai an samu tantama kan Atiku da Peter Obi wajen shiga ADC, duk da hadakar ‘yan adawa da suke jagoranta a jam’iyyar, wacce suke fatar neman tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2027.

Mun yi nadamar yekuwar a ba Yilwatda shugabancin APC – Kungiyar magoya bayan jam’iyyar na Arewa ta tsakiya

1

Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a Yankin Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta bayyana nadamarta bayan ta dage kai da fata sai an naɗa dan yankin a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa.

An dai ware kujerar shugaban APC na ƙasa ga Arewa ta Tsakiyar Nijeriya a taron jam’iyyar na 2022, abin da ya haifar da fitowar tsohon Gwamnan Nasarawa, Adamu Abdullahi. Amma bayan murabus ɗinsa a 2023 ba tare da kammala wa’adin ba, sai aka naɗa Abdullahi Ganduje, tsohon Gwamnan Kano daga Arewa maso Yamma, a matsayin shugaban jam’iyyar.

Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiyar Nijeriya wadda ta ƙunshi manyan jiga-jigan jam’iyyar daga jihohin yankin, ta yi zanga-zanga, tarurruka, taron manema labarai da bayanai domin ganin an mayar da kujerar ga yankin. A ƙarshe, a ranar 24 ga Yuli, 2025, aka naɗa Farfesa Nentawe Yilwatda daga Jihar Filato a matsayin shugaban jam’iyyar.

Sai dai yanzu kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC Forum ta ce Yilwatda ya gaza nuna ƙwarewar jagoranci.

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da Shugabanta, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar a Abuja.

Kungiyar tarayyar Turai za ta tallafa ma gwamnatin Nijeriya da Yuro miliyan 45 don inganta fasahar zamani

0

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) tare da abokan huldarta sun kaddamar da sabon mataki na hanzarta sauyin fasahar dijital a Nijeriya, yayin taron kwamitin kula da cibiyar sauyin fasaha da aka gudanar a Kano, kana aka bude Women Venture Studio Innovation Hub.

A cikin shirin, EU za ta bayar da karin tallafin Yuro miliyan 45 ga shirin 3MTT na gwamnatin tarayya, wanda ke da nufin horas da ‘yan Nijeriya miliyan uku a fannoni na zamani kamar AI, tsaron yanar gizo da kirkirar manhajojin komfuta.

Shugabar sashen Green and Digital Economy na EU, Inga Stefanowicz, ta ce manufar ita ce tabbatar da cewa cigaban fasaha ya kasance na kasa baki daya, inda ta jaddada cewa nan da 2025 za a fadada horo da bunkasa fasahar zamani a dukan sassan Nijeriya.

Zargin El-Rufa’i na biyan ‘yan bindiga Naira biliyan daya ba gaskiya ba ne – Gwamnatin Kaduna

0

Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta zargin da tsohon gwamna jihar, Nasir El-Rufa’i ya yi a Channels TV cewa gwamnatin Uba Sani ta biya ’yan bindiga Naira biliyan 1, tana mai cewa maganar ba ta da tushe balle makama. Wannan na cikin sanarwar da ma’aikatar tsaro ta cikin gida ta fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya riga ya ƙaryata irin waɗannan kalamai tun da, yana tabbatar da cewa babu wata gwamnati da ke biyan kuɗi ga masu laifi. Ta kuma ce El-Rufa’i bai taɓa gabatar da takarda ko wata hujja da ke jaddada zancensa ba.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa gwamnatin Uba Sani na aiwatar da dabarar tsaro mai dogaro da al’umma, tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya, ba ta kuma taɓa tattaunawa ko biyan kuɗi ga ’yan bindiga ba.

Sanarwar ta ce idan El-Rufa’i na da hujja kamar na bayanan banki ko takardun gwamnati ya fito da su cikin sati guda, in ba haka ba a ɗauki matakin doka. Ta ƙara da cewa gwamnatin Kaduna ba za ta bari siyasa ta rikita ci-gaban tsaro da ta fara yin nasara a kai ba.

Dalibai 50 cikin daliban jihar Neja da aka sace sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane – Kungiyar CAN

0

Dalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace a makarantar St. Mary’s Secondary and Primary School da ke Papiri a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja sun tsere daga hannun ’yan bindiga kuma sun koma gidajensu lafiya.

A cewar shugaban Kungiyar Kiristoci Nijeriya reshen jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mamallakin makarantar, waɗannan daliban sun kuɓuta ne a ranar Asabar kuma aka haɗa su da iyalansu, kamar yadda sanarwar sakatariyarsa ta bayyana a ranar Lahadi kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Rev. Yohanna ya ce makarantar na da ɗalibai 430 a aji na firamare, inda 377 suke na kwana. Ya ce yanzu haka, bayan waɗanda suka tsere, dalibai 236, 14 na sakandare da ma’aikata 12 na nan a hannun ’yan bindiga, yayin da hukumomin tsaro ke ƙoƙarin ceto su.

Sojojin Nijeriya sun kama wani da ake zargi da satar mutane inda yake neman kudin fansa Naira miliyan 20 a jihar Taraba

0

Sojojin birget na 6 na rundunar sojin Nijeriya sun kama wani da ake zargi da satar mutane mai suna Umar Musa Geyi, a Wukari da ke jihar Taraba a ranar 22 ga watan Nuwamba 2025, yayin da ake zargin yana neman kudin fansa na Naira miliyan 20 daga iyalan wanda aka sace.

Ana zargin wanda aka kama yana da hannu a sace Alhaji Jano, wani Bafulatani mazaunin Jandei–Kulala, wanda aka sace a ranar 13 ga watan Nuwamba, kuma har yanzu yana hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Kwamandan birget na 6, Birgediya-Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba wa sojojin kan kwarewarsu, inda ya jaddada kudurin rundunar na karyawa da kawar da dukkan hanyoyin aikata laifuka a jihar.

Kare kai da wasu garuruwan ke yi na kara haddasa matsaloli maimakon magance su a jihar Filato – Rundunar sojin Nijeriya

0

Rundunar Sojin Najeriya ta ce barin al’ummomi su kare kansu daga maƙiya ba ya magance rikice-rikicen da faruwa a jihar Filato, illa ƙara tsananta su.

Babban daraktan hulɗar sojoji da fararen hula, Manjo Janar MA Etsy-Ndagi, ya bayyana haka ne a Jos, yana mai cewa tsarin bai taba haifar da da mai ido ba.

A cewarsa, rikicin manoma da makiyaya ya koma salo na hare-hare da ramuwar gayya, inda kowane ɓangare ke zargin ɗaya da farauta ko lalata dukiya.

Hakazalika ya ce dole ne a kwace dukkan makamai kowane iri domin a sami zaman lafiya mai ɗorewa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Etsy-Ndagi ya jaddada cewa sojoji ba sa goyon bayan al’ummomi su ɗauki doka a hannunsu, sai dai suna kare garuruwan da ke fuskantar tashin hankali. Ya kuma yi kira ga mazauna Filato da su zauna lafiya su kuma ba ƙungiyoyin tsaro hadin kai.

Za a iya shawo kan matsalolin Arewacin Nijeriya har da na tsaro matukar za a hada kai – Barau Jibrin

0

Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Barau Jibrin, ya ce Arewa na da duk abin da ake bukata domin shawo kan matsalar tsaro idan shugabanni da muhimman cibiyoyi suka tashi tsaye tare da aiki da juna.

Barau ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 25 da kafa kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya, ACF da aka yi a Kaduna kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cewarsa, Arewa na da ƙarfi, jagoranci da albarkatun da za su magance matsalolin tsaro, yana mai cewa haɗin kai da tsari guda ne kawai ake bukata domin maimaita nasarorin da aka samu a wasu yankuna na ƙasar kuma babu abin da zai hana Arewa ta yi hakan idan aka daidaita matsayi.

Sanata Barau, wanda ya wakilci shugaban majalisar dattawa, ya taya ACF murnar cikarta shekaru 25, yana yaba wa rawar da ta taka wajen kare muradun Arewa da tallafawa ci-gaban ƙasa. Ya kuma tuna da jajircewar dattawan da suka kafa kungiyar, wasu daga cikinsu a yanzu sun rasu.

Hakazalika ya kara da cewa rahoton da jagorancin ACF ya gabatar kan karuwar rashin tsaro da gibin ci gaba bai kamata ya rufe tarihin juriyar Arewa ba, wadda ta dade tana nuna ƙarfin hali da haɗin kai a lokutan ƙalubale.

Gwamnatin jihar Kebbi ta rufe dukkanin makarantun gwamnati da masu zaman kansu saboda barazanar tsaro a jihar

0

Gwamnatin jihar Kebbi ta rufe dukkan makarantun sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar saboda karuwar barazanar tsaro.

Hakan ya shafi manyan makarantu na jihar, ban da kwalejin koyon jinya ta Birnin Kebbi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

A cikin sanarwar da kwamishinonin ilimi Halima Bande da Isa Abubakar-Tunga suka fitar, gwamnati ta ce matakin kariya ne bayan hare-hare da garkuwa da ’yan mata a Maga inda suka ce dole ne a tabbatar da lafiyar dalibai da ma’aikata a yanzu.

Matakin ya shafi daruruwan makarantu a kananan hukumomi 21, yayin da iyaye da dama ke cikin fargaba saboda hare-haren da suka auku kwanakin baya.

Abubakar-Tunga ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar tsaro kuma za a sanar da sabon ranar dawowa idan yanayi ya inganta.