DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
Home Blog Page 94

Tinubu ya zabi jakadun Nijeriya a kasashen waje

0

Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane uku ga majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin jakadu na Nijeriya a wasu kasashen waje.

Shugaban majalisar dattawan Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba, inda ya bayyana cewa jerin sunayen farko ya kunshi mutum uku ne kawai.

A cewar Akpabio, sunayen da shugaban kasa ya aika sun hada da Kayode Are daga jihar Ogun, Aminu Dalhatu daga jihar Jigawa sai Ayodele Oke daga jihar Oyo.

Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da gwamnati ke ci gaba da cike guraben diflomasiyya da suka yi saura tun bayan rushe sunayen wadancan jakadu a farkon mulkin Tinubu.

An sake yunkurin yin juyin mulki a Guinea-Bissau

0

Rahotanni sun yi nuni da cewa an sake yunkurin yin juyin mulki a kasar Guinea-Bissau.

 

Wannan ya zo ne bayan da shugaba mai ci Umaro Sissoco Embaló ya bayyana hasashen sa na samun nasara a zaben shugaban kasar da ya gudana a makon da ya gabata da kashi 65 na kuri’u.

 

’Yan jarida da ke ruwaito zabe sun bayyana cewa lamarin tsaro ya taɓarɓare a babban birni, inda aka jiyo karar harbe-harbe a kewayen ofishin hukumar zabe ta kasar (CNE).

Mahaifin dalibai uku da aka sace a Neja ya rasu – Kungiyar CAN

0

Kungiyar mabiya addinin kirista ta Nijeriya ta bayyana cewa wani mahaifi ga dalibai uku cikin wadanda aka sace a Neja ya rasu sakamakon ciwon zuciya.

 

Shugaban kungiyar na arewacin Nijeriya da kuma Abuja Rev. John Hayab shi ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da gidan talabijin na Arise.

 

John Hayab ya ce mahaifin yaran mai suna Mr. Anthony, ya kadu matuka da samun labarin sace ‘ya’yan nasa, dalili kenan da ya haddasa masa bugun zuciya.

 

Ya nuna damuwa da irin halin tashin hankali da iyayen yaran da aka sace a makon da ya gabata suka tsinci kawunan su, musamman a jihohin Kebbi, Kwara da Neja.

 

Sai da har zuwa wannan lokaci jaridar Punch ba ta tabbatar da sahihancin iƙirarin mutuwar mahaifin a sanadiyyar bugun zuciyar ba.

Bai kamata a nuna sakin yaran da aka sace a matsayin nasara ga gwamnati ba – Atiku Abubakar

Madugun adawa a Nijeriya Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin tarayya kan hanyar da aka bi wajen sakin ‘yan matan da aka sace a Kebbi, yana mai cewa bai kamata a nuna shi a matsayin nasara ba, illa hakan na nuna tabarbarewar lamarin tsaron kasar.

A wata sanarwa da ofishin yada labaran Atiku ya fitar a ranar Laraba, ya ce babban abin damuwa shi ne yadda ‘yan ta’adda a halin yanzu ke yawo babu tsoro, suna tattaunawa, suna kuma sa dokoki da suke so a bi.

A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana cewa DSS da sojoji sun bibiyi ‘yan bindigar kai tsaye a lokacin harin, har suka samu damar tattaunawa da su don a sako daliban ba tare da biyan kudin fansa ba.

Sai dai Atiku ya bayyana wannan magana a matsayin kokarin rufe bakin jama’a da kuma juya gazawar gwamnati ta koma nasara.

Mutanen yankin Alaska na Amurka ba za su kara ganin hasken rana ba, sai sabuwar shekarar 2026

0

Masana sun bayyana cewa sakamakon karkata da aka samu daga saman duniya, yankin Arctic, rana ba za ta fito ba a garin Utqiagvik na jihar Alaska na tsawon kwanaki 64 masu zuwa.

Sai dai hakan ba yana nufin za a yi duhu baki daya ba, domin garin zai rika samun wasu awanni na abin da ake kira “hasken asuba na fari” ‘civil twilight’ a turance wato hasken shuɗi mara kaifi da ake gani kafin fitowar rana, kamar yadda shafin Fox Weather ya wallafa.

Malaman makarantun boko a Nijeriya na barazanar tsunduma yajin aiki saboda yawan satar dalibai

Kungiyar malaman makaranta ta Nijeriya NUT ta yi gargaɗin yiwuwar tsunduma yajin aiki a fadin ƙasar, bayan hare-haren makarantun Kebbi da Niger da suka yi sanadin halaka mutum biyu da sace ɗalibai da dama.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta nuna takaicinta na halaka mataimakin shugaban makaranta da jami’in tsaron da ke kula da makarantar, da kuma sace dalibai 25 a jihar Kebbi.

Haka kuma ta yi Allah wadai da sace sama da dalibai 300 da ma’aikata 12 a jihar Niger, tana mai kiran wadannan hare-haren da ta’addanci kuma abin ƙyama.

NUT ta ce dole gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa domin dakile sake faruwar irin wadannan hare-haren, domin a cewarta, hakan na iya jefa tsarin ilimi cikin halaka.

PDP tsagin Wike suna neman a soke taron da PDP tayi a Ibadan

0

Jam’iyyar PDP tsagin Ministan Abuja Nyesom Wike, ta shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, tana neman a soke taron jam’iyyar da aka gudanar a Ibadan ranar 15 da 16 ga Nuwamba, karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde.

Mukaddashin shugaban jam’iyyar na tsagin, Mohammed Abdulrahman, da sakataren jam’iyyar Samuel Anyanwu, su ne masu shigar da karar, inda suke rokon kotu ta ayyana taron na Ibadan a matsayin harantacce tare da hana INEC amincewa da duk wani hukunci da aka yanke a taron.

Karar ta zo ne bayan wasu koke da tsoffin shugabannin jam’iyyar daga jihohi suka shigar, suna zargin cewa gudanar da taron ya saba wa dokokin PDP.

Cikin wadanda suka gabatar da koken akwai Shugaban PDP na Imo, Austin Nwachukwu, na Abia, Amah Abraham Nnanna, da Sakataren PDP na Kudu maso Kudu, Turnah Alabh George.

Za a shirya fim kan tarihin Nana Asma’u, diyar Shehu Dan Fodiyo

0

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’adu Abubakar III, tare da Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari ta Nijeriya sun amince wa wani kamfani ya fara aikin shirya fim kan rayuwa da bajintar Nana Asma’u, fitacciyar malama, mawallafiya kuma mai fafutukar ilimi a karni na 19.

Fim ɗin zai nuna gudummawar da Nana Asma’u, diyar Shehu Usman Ɗan Fodiyo, ta bayar wajen ilmantarwa, karfafa mata da gina ilimin addini, tare da ba da gudummawa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Nijeriya.

Da take karin haske kan aikin, Mai kokarin shirya fim din Hajiya Rahma Abdulmajid ta ce rayuwar Nana Asma’u hujja ce ta tarihi cewa ilimin mata tushensa yana cikin al’adar Arewa da addinin Musulunci, ba wani sabon abu daga waje ba.

Ta ce nuna irin ilimin da Nana Asma’u ta yada zai taimaka wajen karya tunanin cewa karatun mata sabuwar al’ada ce da ba ta dace da yankin Arewa ba. Ta kara da cewa, rashin ilimi na haifar da rauni a zamantakewa, rashin bin addini yadda ya kamata, tsattsauran ra’ayi da kuma amfani da mata wajen siyasa ta hanyar da ba ta dace ba.

‘Yan bindiga sunkai hari tare da sace mutane a Tsanyawa,jihar Kano

0

‘Yan bindiga sun kai hari tare da sace mutane a ƙauyen Biresawa da ke cikin ƙaramar hukumar Tsanyawa ta jihar Kano.

Lamarin ya faru ne daren Litinin, tsakanin ƙarfe 11 na dare zuwa 12 na dare.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa akalla mutane takwas aka yi awon gaba da su maza biyu da mata shida, har ya zuwa wannan lokaci ba a samu labarin inda aka kai su ba.

Majiyar ta ce maharan sun shiga ƙauyen ne dauke da bindigogi, ta kuma bayyana cewa mazauna yankin sun shai da wa jami’an tsaro tun kafin faruwar harin bayan samun rahoton wasu baƙin duskoki da suka shiga yankin.

A wasu ƙauyuka kamar Sarmawa, Yan Chibi da Gano ma an tabbatar da sace mutane fiye da goma yayin da kusan ‘yan bindiga 50 kan babura suka yi dirar mikiya a garuruwan.

Ganduje na shirin kafa sabuwar kungiyar sa-kai mai kama da Hisbah

0

Tsohon Shugaban jam’iyar APC a Nijeriya Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da shirin kafa wata sabuwar ƙungiya mai kama da Hisbah, karkashin Cibiyar Ganduje Foundation domin karɓar ma’aikatan Hisbah 12,000 da gwamnatin jihar ta sallama daga aiki.

Wannan na zuwa ne bayan Ganduje ya karɓi rahoton kwamitin tantance waɗanda aka sallama daga aiki.

Jaridar Daily Trust ta rawaito Ganduje na bayyana sallamar a matsayin rashin adalci kuma abin da ya tilasta nemo musu mafita.

Da yake jawabi ga kwamitin da Gandujen ya kafa kan batun, ya ce sabuwar rundunar da za a yi za ta kasance mai zaman kanta da za ta ba da dama ga duk wanda ya ke son shiga ciki har da waɗanda ba su kasance cikin mutum 12,000 ɗin da aka sallama.

Ya bayyana cewa tsohon Kwamandan Hisbah, Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina shi ne zai jagoranci aikin kafa wannan runduna, wacce za ta yi aiki irin na Hisbah, ciki har da wayar da kai, taimakon gaggawa, yi wa jama’a nasiha da kuma taimako a lokutan bukata.