Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana damuwarsa bisa yawaitar hare-hare, kisa da kuma garkuwa da mutane da ake fuskanta a jihohin ƙasar nan, musamman Kebbi da Zamfara.
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi tir da yawaitar tashe-tashen hankula a fadin Nijeriya, musamman hare-haren da ake yi da kuma garkuwa da mutane da dama a jihohin Kebbi da Zamfara.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yana Allah wadai da abin bakin cikin, Pantami ya yi kira ga hukumomin gwamnati da su gaggauta rungumar sabbin dabaru na zamani da suka dogara ga fasaha domin yakar ta’addanci da kuma kare rayukan ‘yan kasa.
Pantami ya ce amfani da fasahohi na zamani zai taimaka wajen cafke masu aikata laifin, hana sake faruwar irin wadannan hare-hare, da kuma dawo da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci ’yan kasa su rika bada bayanan sirri da zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen tunkarar miyagun laifuka.
