Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaPDP ta gargadi ‘yan jam’iyyar da ke goyon bayan Tinubu ya yi...

PDP ta gargadi ‘yan jam’iyyar da ke goyon bayan Tinubu ya yi tazarce a wa’adi na biyu

Jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ta yi gargadi mai tsanani tare da jan kunnen mambobinta da ke yi wa jam’iyyar zagon kasa, da ta kira maciya amana musamman waɗanda ke mara wa Shugaba Bola Tinubu baya.

Mai magana da yawun jam’iyyar PDPin a Najeriya, Debo Ologunagba ya ce abin damuwa shi ne ci gaba da fitowa a kafafen yaɗa labarai da sukar jam’iyyar da wasu fitattun mambobi ke yi, da ayyukansu da kalamansu.

Daga cikinsu, ya ce har da bayyana goyon bayansu da kuma niyyar yin aiki domin nasarar jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, abin da ya ci karo da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin PDP na 2017 da aka yi wa gyaran fuska.

Ya ambato Sashe na 10 (6) na Kundin PDP, wanda ya ce “Babu wani memba na jam’iyya da zai haɗa kai da wata jam’iyya ko ƙungiya domin yi wa jam’iyya ko gwamnatin da aka kafa karkashin jam’iyyar zagon kasa”

Debo Ologunagba ya kara da cewa wannan lamarin, babbar barazana ce ga zaman lafiya da dorewar jam’iyyar su, domin ya na janyo rarrabuwar kai, rashin jituwa da kuma korar wasu mambobi cikin jam’iyyar.

Kwamitin gudanarwa na kasa na jam’iyyar PDP ya bukaci dukkan mambobin jam’iyyar su dawo kan hanya ko kuma su fuskanci hukunci mafi tsauri da doka ta tanada.

Hakama PDPn ta bukaci dukkan mambobinta su kasance masu biyayya tare da ci gaba da aiki tukuru domin ganin PDP ta gudanar da babban taronta na kasa dake tafe a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025 a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata