Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaPDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam'iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

PDP ta maido wa Samuel Anyanwu mukaminsa na sakataren jam’iyyar na kasa

Jam’iyyar PDP ta dawo da Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na kasa bayan ganawarta da hukumar INEC a ranar Talata.

Shugaban rikon kwarya na PDP, Umar Damagum, ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce Anyanwu zai ci gaba da aiki a matsayin sakataren kamar yadda gidan Talabijin na Channels ya tabbatar.

Jam’iyyar ta kuma soke taron NEC da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga Yuni, inda ta maye gurbinsa da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

A baya hukumar zaben Nijeriya INEC ta ce ba za ta halarci taron NEC na PDP ba saboda rikicin shugabancin sakataren jam’iyyar da kuma sabanin da ke cikin sa hannun takardun da aka aikewa hukumar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata