Kwamitin zartaswa na Ƙasa na jam’iyyar PDP ya musanta zargin ƙirƙirar sa hannu da Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya yi.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja a ranar Litinin.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito Ologunagba ya mayar da martani ne kan ikirarin Anyanwu cewa an ƙirƙiri sa hannunsa a cikin takardun da aka aika wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) don sanar da ita rana, lokaci, da wurin gudanar da taron gangamin jam’iyyar da aka shirya yi a ranar 15 da 16 ga Nuwamba a Ibadan, Jihar Oyo.
Sai dai Ologunagba ya nace cewa Sakataren ƙasa da kansa ne ya sanya hannu a takardun.
Tuni dai Anyanwu ya riga ya kai ƙorafi ga Hukumar Tsaro ta DSS da kuma Sufeton Ƴan Sanda na Ƙasa, yana zargin cewa an ƙirƙiri sa hannunsa.
