Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiPDP ta sauya wurin taron kwamitin amintattu zuwa Yar’Adua Centre

PDP ta sauya wurin taron kwamitin amintattu zuwa Yar’Adua Centre

Jam’iyyar PDP ta sauya wurin taron Kwamitin Amintattu (BoT) daga Sakatariyar ta ta kasa da ke Wadata Plaza, Abuja, zuwa Cibiyar Yar’Adua da ke unguwar kasuwanci ta Abuja, bayan da ‘yan sanda suka hana su shiga sakatariyar.

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar a shafinta na X, PDP ta bukaci mambobin BoT su nufi sabon wurin taron, tana mai zargin ‘yan sandan da nuna danniya da kuma hana shiga sakatariyar bisa wani umarni daga sama.

Wasu mambobin BoT da suka hada da Maina Chiroma da tsohon sakataren jam’iyyar, Umar Tsauri, sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun hana su shiga harabar sakatariyar. Taron na BoT da kuma na NEC na yau sun haifar da sabbin takaddama a cikin jam’iyyar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata