Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaPDP za mu ji da matsalolin mu – Martanin Saraki ga kalaman...

PDP za mu ji da matsalolin mu – Martanin Saraki ga kalaman Tinubu kan ‘yan adawa na ranar dimokradiyya

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dr. Bukola Saraki, ya amsa jawabin Shugaba Bola Tinubu kan rikicin jam’iyyun adawa, yana mai cewa PDP na da matsaloli, amma za su gyara jam’iyyarsu da kansu.

A rahoton da jaridar Punch ta fitar, Saraki yace dole su karɓi maganar Tinubu yadda take, amma ba ya goyon bayan jam’iyya guda, a sakamakon haka za su gyara gidajensu da kansu

Saraki ya ce PDP da sauran jam’iyyun adawa za su mayar da hankali kan sake tsari da haɗa kan jama’a, musamman ganin babu matsin lamba daga gwamnati.

A ranar Alhamis yayin Ranar Dimokuraɗiyya, Shugaba Tinubu ya ce yana jin daɗin rikice-rikicen da ke faruwa a jam’iyyun adawa, tare da karyata zargin cewa yana kokarin kafa jam’iyya ɗaya tilo a ƙasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata