Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaPDP za ta tsayar da Kirista takarar shugaban kasa daga Kudu –...

PDP za ta tsayar da Kirista takarar shugaban kasa daga Kudu – Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP za ta tsayar da ɗan takarar shugaban kasa daga Kudancin Najeriya wanda yake Kirista a zaɓen 2027.

Mohammed ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels T ranar Alhamis.

Ya ce PDP ta koyi darasi daga kuskuren da jam’iyyar APC ta yi a zaɓen 2023, lokacin da ta tsayar da tikitin addini ɗaya (Muslim-Muslim ticket).

Gwamnan Bauchi ya kuma musanta jita-jitar da ke cewa PDP na shirin tsayar da gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa tare da sanya shi a matsayin mataimaki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata