Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiPENGASSAN ta tsunduma yajin aiki a Nijeriya

PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki a Nijeriya

An shiga sabon rikici tsakanin ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN da kamfanin Dangote Refinery, bayan da ƙungiyar ta bayar da umarnin tsunduma yajin aiki a fadin kasar sakamakon korar ma’aikata sama da 800 da ta yi zargin matatar man Dangote ta yi.

PENGASSAN ta bayyana cewa korar ɗimbin ma’aikata a kamfanin ba bisa ka’ida ba ne, tana mai cewa hakan ya saba wa haƙƙin kwadago kuma yana iya zama babbar barazana a nan gaba.

A cikin wata sanarwa,, ƙungiyar ta zargi kamfanin da korar ‘yan Najeriya saboda sun shiga kungiyar PENGASSAN, tare da maye gurbinsu da ƙarin ma’aikata ‘yan ƙasashen waje fiye da 2,000.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata