Magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi sun yi wa Atiku Abubakar raddi game da kalamansa na ba zai janye wa wani dan takara ba a fafatukar samun tikitin takarar shigabanci kasa a jam’iyyar ADC ba.
A cewarsu, dan takararsu ba zai zama cikin siyasar sayen kuri’un masu zaben fidda gwani ba.
Da yake magana da jaridar Punch, kodinatan kungiyar magoya bayan Obi na kasa, Dr Yunusa Tanko ya ce, tsarin siyasar Peter Obi ya sha bamban da na saura da ke amfani da kudi a siyasa.
Kazalika ya ce, ya ji dadi da Atiku ya bayyana abin da ke a zuciyarsa wanda za su iya kafa hujja da shi amma Peter Obi zai kawo sauyi a tsarin siyasar Nijeriya.
