Monday, April 6, 2026
HomeSiyasaPeter Obi na da 'yancin yi wa jam'iyyar Labour takara a 2027...

Peter Obi na da ‘yancin yi wa jam’iyyar Labour takara a 2027 da ni ko da wani – Datti Baba Ahmed

Sanata Yusuf Datti Baba Ahmed da ya yiwa Peter Obi takarar mataimaki a zaben 2023 karkashin jam’iyyar Labour Party yace, Obi nada damar tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar koda kuwa ba shine zai masa mataimaki ba a zaben 2027 da ke tafe.

Baba Ahmed yayi kalaman nasa ne a yayin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels, inda yace Mutane biyu ne yake da matukar girmamawa a gare su kuma daya daga cikin su shi ne Peter Obi

Yakara da cewa hulda da gamayyar jam’iyyu da Peter Obi ke yi a karkashin inuwar ADC ba cin amanar jam’iyya ba ne, illa dai wani sabon yanayi da siyasar Nijeriya ta shiga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata