Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiPeter Obi na iya lashe kuri'un Arewacin Nijeriya idan ya koma PDP,...

Peter Obi na iya lashe kuri’un Arewacin Nijeriya idan ya koma PDP, in ji Jerry Gana

Ɗaya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP, Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa Peter Obi zai kayar da kowane dan takara a jihohin Arewa matukar ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar PDP.

Yayin wata hira da yayi a Arise TV, Farfesa Gana ya ce binciken ra’ayoyin jama’a da ya gudanar ya nuna cewa mutanen Arewa masu adalci ne, kuma suna ganin Peter Obi a matsayin dan takara mai gaskiya da nagarta.

A shekara ta 2022, Peter Obi ya bar jam’iyyar PDP domin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Labour Party, inda ya yi fice sosai a zaben 2023.

Farfesa Gana ya kuma tunatar da ’yan Najeriya cewa jam’iyyar PDP ta kafa turba mai kyau tun daga lokacin da ta taimaka wajen dawo da mulkin dimokuradiyya a 1999.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata