Monday, April 6, 2026
HomeWasanniRooney ya caccaki Manchester United kan rashin ci gaba a zamanin Ruben...

Rooney ya caccaki Manchester United kan rashin ci gaba a zamanin Ruben Amorim

Tsohon kyaftin din Manchester United kuma wanda ya fi zura kwallaye a tarihin kungiyar Wayne Rooney, ya bayyana cewa ƙungiyar ta ƙara lalacewa a ƙarƙashin mai horaswa Ruben Amorim.

Rooney ya yi waɗannan kalamai ne bayan Manchester United ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Manchester City a wasan makon da ya gabata a gasar Firimiya ta kasar Ingila.

Ya ce duk da cewa ya na son ya nuna goyon baya ga kocin da ’yan wasan, amma babu wani alamar cigaba da ake gani a cikin tsarin kungiyar.

Ya kara da cewa babu wani tsarin da ke nuna za a samu sauyi a kungiyar nan gaba, kullum al’amura ƙara tabarbarewa suke.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata