Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiRukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya-...

Rukunin farko na maniyyatan jihar Bauchi a Nijeriya, sun tashi zuwa Saudiyya- NAHCON

Hukumar aikin Hajji ta Nijeriya ta bayyana cewa maniyyata 2,520 ne daga cikin jihar Bauchi za su halarci aikin Hajjin bana na 2025 a kasar Saudiyya, domin sauke farali.

jaridar the Cable ta rawaito cewa a yayin bikin bankwana da aka shirya a cibiyar Alhazai ta Sultan Sa’ad da ke Bauchi, Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed, ta bakin Mataimakinsa, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ya shawarci mahajjatan da su yi amfani da lokacinsu wajen ibada da neman rahamar Allah a kasa mai tsarki.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta dauki nauyin shirya masauki mai inganci wanda ke kusa da Masallacin Harami tare kuma da tabbatar da cewa duk wani shiri da ya shafi kiwon lafiya, sufuri da kula da lafiyar mahajjata ya kammala, domin tabbatar da ingantaccen aikin hajji.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata