Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiRundunar ƴan sandan Delta na tuhumar jami’anta da karbar na goro

Rundunar ƴan sandan Delta na tuhumar jami’anta da karbar na goro

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Delta ta tabbatar da kama wasu jami’anta da suka bayyana a bidiyo suna lissafin dimbin kuɗi a cikin motar sintiri mai alamar Area Command Asaba.

Bidiyon ya bazu a shafukan sada zumunta, inda jama’a suka yi zargin cewa kuɗin na iya zama irin na goro da wasu jami’ai kan karba a manyan hanyoyi ko na kwace.

Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun rundunar, Bright Edafe, ya tabbatar da cewa an gano jami’an, an gurfanar da su gaban kwamishinan ’yan sanda, sannan an ɗauki matakin dakatarwa da tsarewa.

Ya ce tuni rundunar ta tura manyan jami’an biyu sashen tuhuma, yayin da sauran su biyun, masu mukamin Inspector kuma ake tsare da su don fuskantar shari’a a cikin gida, wacce ke matsayin tsarin ladabtarwa a rundunar.

RELATED ARTICLES

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata