Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation Fasan Yamma ta tabbatar da ajalin sanannen shugaban ‘yan ta’adda, Yellow Danbokkolo, a wani kazamin samame da ya dauki mako guda a yanking Arewa maso Yamma.
Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja, inda ya ce an kaddamar da aikin hadin gwiwa da hadakar dakaru, jiragen yaki da kuma wasu hukumomin tsaro, bayan samun sahihin bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’addan da ke tserewa.
Kangye ya ce Danbokkolo ya shahara wajen shan miyagun kwayoyi irin su pentazocine domin kara karfin aikata ta’asa da salwantar da rayuka da ya yi kaurin suna wajen aikatawa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
