Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiRundunar sojin sama ta Nijeriya ta yi ajalin 'yan bindiga sama da...

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta yi ajalin ‘yan bindiga sama da 100 a dajin Zamfara

Rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) tare da hadin gwiwar sojojin kasa sun kawo karshen sama da ’yan bindiga 100 a wani samame na hadin gwiwa da aka gudanar a safiyar Lahadi a Dajin Makakkari, karamar hukumar Bukuyum, jihar Zamfara.

Samamen ya hada da luguden wuta daga jiragen yaki na NAF sannan sojojin kasa suka ci gaba da aikin kakkabe maboyar ’yan bindigar, inda suka lalata babura da dama tare da rusa sansanoninsu.

Rahotannin da jaridar Then Nation ta tattaro sun nuna cewa tsawon makonni, jami’an leken asiri na Operation FANSAN YAMMA (OPFY) suna bin diddigin motsin ’yan bindiga a yankunan Sunke, Kirsa da Barukushe, wadanda aka dade ana bin diddigin su na zama mafakar ’yan ta’adda a jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata