Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiRundunar 'yan sanda ta kama mutane 53 kan tagwayen hare-hare a jihohin...

Rundunar ‘yan sanda ta kama mutane 53 kan tagwayen hare-hare a jihohin Benue da Filato – IGP Egbetokun

Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa an kama mutane 53 da ake zargi da hannu a hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a jihohin Benue da Filato.

Ya ce an kama mutum 26 dangane da harin Yelewata a Benue, sa’annan sai wasu 22 a Plateau, da kuma karin wasu 5 a Benue.

Harin Yelewata ya yi sanadin salwantar rayukan mutane 47 da raunata 27, yayin da aka kwato bindigogi kirar AK-47 guda 8 da bindigogi nau’in GPMG guda 2.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata