Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiRuwan sama da iska mai karfi ya rusa gidan wasu sabbin ma'aurata...

Ruwan sama da iska mai karfi ya rusa gidan wasu sabbin ma’aurata a Katsina

Akalla gidaje 300 ne suka rushe, tare da asarar dukiyoyi da darajarsu ta haura miliyoyin Naira, sakamakon wani hadari mai karfi tare iska da aka samu tare da ruwan sama a wasu unguwanni a birnin Katsina.

Lamarin da ya dauki kusan mintuna goma sha biyar da yamma bayan sallar La’asar a ranar Laraba, ya haddasa kwarewar rufin gine-gine kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

Daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa akwai Sabuwar Unguwar Modoji, Shinkafi, da yankin Kukar-Gesa, har da Ambassador Quarters da kuma wasu sassan karamar hukumar Jibia.

Mutane da dama, ciki har da wasu sabbin ma’aurata, sun rasa matsugunansu sakamakon wannan iftila’i.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata