Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiSabbin nade-naden Tinubu ba su kawar da kyamar da yake nuna wa...

Sabbin nade-naden Tinubu ba su kawar da kyamar da yake nuna wa arewa ba – Mahadi Shehu

Ga videon wannan rahoto: 

 

Ruwan
mukamai ne dai Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa mutanen da suka fito daga
arewacin Nijeriya a baya-bayan nan. Kama daga jagorancin hukumar alhazai ta
kasa zuwa hukumar PTDF wadda ke tura matasan Nijeriya karatu kasashen ketare ta
amfani da  rarar kudaden da gwamnati ta
samu a harkar man fetur zuwa hukumar NCC mai sanya ido kan harkoki na sadarwa
da kuma hukumar ICPC mai yaki da rashawa a Nijeriya, dukkaninsu Shugaba Tinubu
ya damka su a hannun mutanen arewa. Sai dai a cewar, Mahadi Shehu, wanda ya jima
yana zargin gwamnatin Tinubu da fifita kabilar Yarbawa a wajen nada mukamai,
wadannan nade-nade ba su gyara kyamar da Mahadin ke zargin Tinubu da nuna wa
mutanen arewa ba.

Sai dai
gwamnatin Tinubu ta ce babu adalci a cikin irin wannan fahimta ta Mahadi Shehu.
Abdulaziz Abdulazi da ke magana da yawun Shugaba Tinubu ya ce zafin shan kaye a
zabe ne ke sanya irinsu Mahadi Shehu sukar gwamnatin ta APC.

Duk da cewa
tun a zamanin mulkin mallaka ne dai manyan kabilun Nijeriya suka fara nuna wa
juna rashin amincewa a wajen rabon mukami, har yanzu matsalar taki ci, taki cinyewa,
a cewar Ibrahim Baba Shatambaya, malamin jami’ia da ke  sharhi a kan lamurran siyasa a Nijeriya.

A yayin da
masu adawa da salon nade-naden gwamnatin Tinubu ke ci gaba da matsa mata lamba,
masu sharhi na aza ayar tambaya a kan, shin mutanen arewa suke son  gani a shugabanci ko da  ba za su iya tabuka wani abu ba ko kuwa
mutanen da za su kawo ci gaba a Nijeriya, tun da a baya an ba ‘yan arewa
mukamai masu gwabi kuma ba a ga wani cci-gaba ba?

Masu sharhi
dai sun tsura ido su ga ko wadanda Shugaba Tinubun ya nada mukamai dabam-dabam
za su tabbatar da zargin ‘yan adawa na danne yankin arewacin Nijeriya a wajen
zuba ayyukan gwamnati ko kuma za su bai wa mara da kunya.

 

DCL Hausa

Aisha Usman
Gebi

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata