Sunday, April 5, 2026
HomeLabarai'Sabis' din MTN ya dawo a jihohin Kano, Adamawa da Borno, bayan...

‘Sabis’ din MTN ya dawo a jihohin Kano, Adamawa da Borno, bayan wasu gyare-gyare da kamfanin ya gudanar

Kamfanin sadarwa na MTN yabayyana cewa ya kammala aikin gyaran hanyar sadarwar da ya shafi rukunin sadarwa guda 101 a cikin kananan hukumomi 15 na jihohin Adamawa, Borno da Kano.

Kamfanin sadarwar ya fitar da sanarwa a ranar Litinin cewa maido da hanyoyin ya kasance babban mataki a ci gaban kokarinsa na inganta sahihancin ‘sabis’ a yankin Arewa maso Gabas, duk da yawan matsalolin yankan layin fiber da kuma barna.

Aikin gyaran, wanda aka gudanar a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, ya haɗa da sauya hanyar zirga-zirgar sadarwa zuwa sabon layin fiber da aka girka a kan hanyar AFCOT–Bawo Village a Jihar Adamawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata