Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta ƙara tsaurara sa ido da binciken lafiya a dukkan iyakokin ƙasar, tashoshin ruwa da filayen jiragen sama domin dakile yiwuwar shigowar cutar Ebola daga Jamhuriyar dimokuraɗiyyar Congo.
Ma’aikatar lafiya ce ta sanar da hakan ta bakin Dr. Akpan Nse, inda ya ce an ɗauki ƙarin ma’aikata tare da tallafin hukumar lafiya ta duniya WHO da wasu kamfanoni masu zaman kansu domin tabbatar da aikin da kuma inganta na’urorin duba zafin jiki a filayen jiragen sama.
A cewar sa, duk fasinjojin da suka shigo Nijeriya daga Congo ko waɗanda suka bi ta can za a yi musu cikakken bincike tare da cike fom ɗin bayanan lafiya kafin izinin shiga ƙasar.
