DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, April 11, 2026
HomeLabaraiSanata Barau ya gana da gwamnan Edo kan hallaka matafiya a Uromi,...

Sanata Barau ya gana da gwamnan Edo kan hallaka matafiya a Uromi, yayin da ake shirin tura wadanda aka kama zuwa Abuja

 

Gwamna jihar Edo Monday Okpebholo ya kai ziyarar jaje ga mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin bisa hallaka matafiya a garin Uromi da ke jihar Edo a makon da ya gabata.

Mataimaki na musamman ga Sanata Barau kan harkokin yada labarai Alhaji Ismail Mudashir, ya ce gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga mataimakin shugaban majalisar, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar Edo za ta taimaka wa iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Gwamnan jihar Edo ya bayyana cewa mutane 14 da ake zargi da hannu a kashe matafiyan da ba su ji ba ba su gani ba, ana shirin kai su a Abuja domin ci gaba da yi musu tambayoyi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata