Sanata Agom Jarigbe mai wakiltar mazabar Arewa ta jihar Cross River ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya sanar da majalisar dattawa ta hanyar aika wasiƙa a hukumance.
A yayin zaman majalisar da aka watsa kai tsaye a NASSTV a ranar Talata, mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin, ya karanta wasiƙar ficewar sanatan, inda Jarigbe ya ce rikice-rikicen cikin gida a PDP ne suka tilasta masa daukar matakin ficewar.
Jarigbe ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tunani mai zurfi kan halin da jam’iyyar ta tsinci kanta a matakin jiha da kasa, inda ya koka da rarrabuwar kawuna da rashin sulhu a cikinta.
A cewarsa, jam’iyyar APC ce ke ba shi cikakken dandali na ci-gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani al’ummar mazabarsa.
