Sunday, April 5, 2026
HomeSiyasaSanata Rufa'i Hanga ya nemi a dawo da motocin da ya raba...

Sanata Rufa’i Hanga ya nemi a dawo da motocin da ya raba don aikin NNPP

Sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga ya nemi shugabannin kananan hukumomin yankinsa su dawo da motocin da ya ba su bayan ficewar su daga NNPP.

Wata sanarwa da ofishin Sanatan ya fitar, ta yi nuni da cewa tun da fari an raba wa shugabannin kananan hukumomin da ke yankin Kano ta tsakiya motocin ne don gudanar da ayyuka da suka shafi jam’iyyar NNPP, gabanin sauyin da aka samu a fagen siyasar Kano.

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC bayan ficewa daga NNPP tare da daukacin shugabannin kananan hukumomin Kano da wasu yan majalisar dokokin jiha da na tarayya.

Kananan hukumomin da umarnin ya shafa sun hadar da Dala, Dawakin Kudu, Fagge, Garun Mallam, Gezawa, Gwale, Kano Municipal, Kumbotso, Kura, Madobi, Minjibir, Nasarawa, Tarauni, Ungogo da kuma Warawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata