Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bukaci hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci su gudanar da cikakken bincike kan wa’adin shekaru takwas na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin almundahana da cin zarafi.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito cewa Shehu ya yi wannan kira ne yayin taron manema labarai a Kaduna, inda ya bukaci hukumomin su binciki abin da ya kira karkatar da kudaden al’umma da suka kai daruruwan biliyoyin naira a tsakanin 2015 zuwa 2023.
Ya kuma yi kira ga hukumar yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta Nijeriya EFCC, da ta dauki mataki kan rahotannin da majalisar dokokin jihar Kaduna ta fitar na zargin aikata ba daidai ba, domin tabbatar da adalci.
