Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiSanata Wadada, ya fice daga jam’iyyar SDP

Sanata Wadada, ya fice daga jam’iyyar SDP

Sanata mai wakiltar Nassarawa ta Yamma Ahmed Wadad ya fice daga jam’iyyar SDP.

Wannan na kunshe ne a wata wasika da ya aika wa shugaban jam’iyyar na Tudu Ward, ta karamar hukumar Keffi, wacce aka bai wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN.

A cikin wasikar, Wadada ya ce ya dauki wannan mataki ne saboda rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar na tsawon lokaci, wadanda suka janyo rabuwar kawuna da kuma shari’o’i.

Wadada ya kuma nuna yiwuwar komawa jam’iyyar APC, inda ya taba zama kafin ya koma PDP, sannan daga baya ya koma SDP.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata