Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiSarkin Daura ya tsige dagaci kan zargin sace mata da fyade

Sarkin Daura ya tsige dagaci kan zargin sace mata da fyade

Sarkin Daura, Alhaji Faruq Umar Faruq, ya tsige Iliya Mantau, Dagacin Mantau a karamar hukumar Baure, bisa zarginsa da hannu wajen sace wata mata da jaririyarta tare da yi mata fyade.

Tsige shi ya biyo bayan zanga-zangar matasa da korafe-korafen da mazauna garin Yarmaulu suka shigar, inda aka zargi Dagacin da wasu da laifin garkuwa da Zulaihatu da karbar kudin fansa N20m kafin yi mata lalata.

Lamarin da ya jima yana gaban kotu, ya janyo ce-ce-ku-ce saboda jinkirin daukar mataki daga masarauta na tsawon kusan shekara guda.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata