Jami’ar Northwest da ke a Kano ta amince da ba Sarkin Kano, Dakta Muhammadu Sanusi II, gurbin karatu na musamman a shirin LL.B (Common Law da Shari’a).
Wata wasiƙa mai kwanan wata 12 ga Janairu, 2026, wadda shugaban sashen jarrabawa da shigar dalibai na jami’ar, Jafaru Muhammad, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa an ba Sarkin gurbin ne bayan ya cika sharuddan da ake bukata na shiga ta musamman.
Wasiƙar ta ce za a fara karɓar Sarkin a mataki na 200 a Kwalejin Shari’a, tun daga zangon karatu na 2024/2025, kuma dole ne ya bi duk ƙa’idojin da ke cikin kundin dokokin dalibai na jami’ar.
Jami’ar ta kuma bukaci Sarkin da ya kammala rajistarsa ta hanyar gabatar da kansa ga sassa daban-daban da suka hada da sashen shigar dalibai, ICT, asusu, ɗakin karatu da kuma sashen harkokin dalibai.
