Ƙungiyar da ke fafutikar kare hakkin bil’adama a Nijeriya SERAP ta shigar da ƙara a gaban kotu kan gwamnonin jihohi da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, bisa zargin gaza yin bayani kan biliyoyin naira da aka kashe a matsayin kuɗaɗen tsaro (security votes) tun daga 29 ga Mayu, 2023.
A cewar SERAP, an shigar da ƙarar ne sakamakon ci gaba da tabarbarewar tsaro a jihohi da dama da kuma birnin taraiyar Nijeriya Abuja, duk da manyan kuɗaɗen jama’a da ake warewa duk shekara don tsaro.
Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da ta bayyana shigar da ƙarar, wacce Mataimakin Daraktan SERAP Kolawole Oluwadare ya sanya wa hannu kuma aka miƙa wa PUNCH Online a ranar Lahadi.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/95/2026, wacce aka shigar a Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Juma’ar da ta gabata, SERAP na roƙon kotu ta tilasta wa gwamnonin jihohi da Ministan Abuja su bayyana a bainar jama’a yadda aka kashe kuɗaɗen tsaro da suka karɓa tun daga 29 ga Mayu, 2023.
Ƙungiyar ta kuma nemi kotu da ta bayar da umarni da zai sa su gabatar da cikakkun rahotanni kan yadda aka ware, aka yi amfani, matakin aiwatarwa da kammala ayyuka da aka ɗauki nauyinsu da kuɗaɗen tsaro, tare da shirye-shiryen inganta kayayyakin tsaro a jihohinsu da kuma Abuja.
A cewar SERAP, sama da Naira biliyan 400 ake kasafawa duk shekara a matsayin kuɗaɗen tsaro a faɗin Najeriya, yayin da rahotanni ke nuna cewa akalla gwamnonin jihohi 10 sun ware kusan Naira biliyan 140 don wannan manufa a kasafin kuɗin shekarar 2026.
A cikin ƙarar, SERAP ta jaddada cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake amfani da kuɗaɗen jama’a da aka tanada domin kare rayuka da dukiyoyi, musamman a wannan lokaci da matsalar tsaro ke ƙara kamari.

