Kungiyar SERAP ta shigar da kara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da kamfanin NBET, bisa zargin kasa bayyana yadda aka kashe N128bn na kudin jama’a. SERAP ta ce karar ta biyo bayan rahoton Babban Akanta Janar na Tarayya da aka wallafa a ranar 9 ga Satumba, 2025.
A cikin karar, SERAP na neman kotu ta tilasta wa Adelabu da NBET su yi bayani kan abin da ta kira “batan ko karkatar da N128bn,” tare da bayyana ranar fitar da kudaden da kuma wadanda suka amfana. Kungiyar ta kuma bukaci a bayyana sunayen jami’an gwamnati da suka amince ko suka taka rawa wajen sakin kudaden.
SERAP ta ce cin hanci da rashawa a bangaren wutar lantarki na ci gaba da jefa ‘yan Nijeriya cikin duhu, tare da matsalar rugujewar babban layi da hauhawar kudin lantarki. Kungiyar ta ce amincewar kotu da bukatunta zai taimaka wajen inganta gaskiya, da magance matsalolin wutar lantarki a Nijeriya.
