Thursday, April 9, 2026
HomeSiyasaSeyi Tinubu ya kai matsayin neman takarar shugabancin Najeriya - Daniel Bwala

Seyi Tinubu ya kai matsayin neman takarar shugabancin Najeriya – Daniel Bwala

Hadimin shugaban Najeriya Daniel Bwala, ya ce dan gidan shugaban Seyi Tinubu ya kai matsayin da zai iya neman takara a kowane irin mukamin siyasa a Najeriya, ciki kuwa har da kujerar shugaban kasa.

 

Yayin wata tattaunawa da shi da aka wallafa a kafar YouTube, Bwala ya ce batun da ake yi na cewa Seyi ya samu daukaka ta sanadiyyar mahaifinsa ba gaskiya bane, yana mai bayyana shi a matsayin jajirtacce.

 

Kazalika ya ce Seyi Tinubu ya kasance mutum mara girman kai, domin baya kallon girma ko matsayin mahaifinsa yayin gudanar da al’amuransa, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata