Shugaban Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Hon. Tajudeen Abbas, ya bai wa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, tabbacin cewa dukkanin yankunan majalisar dattawa uku na jihar Kaduna sun hada kai suna goyon bayansa da kuma Gwamna Uba Sani a babban zaben 2027 da ke tafe.
Abbas ya bayyana hakan ne a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja, lokacin da ya jagoranci tawagar manyan masu ruwa da tsaki daga Kaduna, ciki har da Sanata Sunday Marshall Katung mai wakiltar Kaduna ta Kudu, da Sanata Shehu Sani wanda ya taba wakiltar Kaduna ta Tsakiya tsakanin 2015 zuwa 2019.
Ya ce ziyarar wata muhimmiyar ganawa ce domin sanar da shugaban kasar yadda jam’iyyar APC ke kara samun karbuwa a fadin jihar Kaduna.
Shugaban majalisar ya jaddada cewa jam’iyyar APC ta samu cikakkiyar karbuwa a dukkan sassan jihar, inda ya tabbatar da cewa zaben 2027 ya kusa zama tabbatacce ga jam’iyyar, tare da samun gagarumar nasara a dukkanin matakai.
A cewarsa, sabanin yadda a baya APC ke da karfi ne kawai a yankunan arewa da tsakiya, yanzu haka sabbin sauye-sauyen siyasa sun sa jam’iyyar ta samu karbuwa har a yankin kudancin jihar, wanda a baya ake dauka a matsayin sansanin PDP.
Ya kara da cewa wannan nasara ta samo asali ne sakamakon yadda Gwamna Uba Sani ke tafiyar da mulki cikin hadin kai da bai wa kowa dama, wanda hakan ya jawo goyon baya daga bangarori daban-daban na addini.
Har ila yau, Abbas ya bayyana cewa sauya sheka da wasu jiga-jigan PDP suka yi, ciki har da Sanata Katung da wasu zababbun jami’ai, ya kara karfafa matsayin APC a duk fadin jihar Kaduna.
