Thursday, April 9, 2026
HomeLabaraiShaye-shayen miyagun kwayoyi na barazana ga makomar Nijeriya

Shaye-shayen miyagun kwayoyi na barazana ga makomar Nijeriya

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Manjo Janar Buba Marwa mai ritaya, ya gargadi matasa kan hatsarin da ke tattare da shaye-shaye, yana mai cewa lamarin na daga cikin manyan abubuwan da ke barazana ga makomar Nijeriya.

Ya bayyana haka ne a Abuja yayin da yake gabatar da jawabi a taron wayar da kan matasa ta hanyar shirya kwallon kafa da kamfanin Richy Gold International Ltd tare da haɗin gwiwar NDLEA suka shirya.

Marwa ya nuna damuwa kan yadda ake samun yawaitar amfani da miyagun kwayoyi kamar taba sigari, giya, wiwi, tramadol, codeine a makarantu da cikin al’umma da ma cikin harkokin wasanni.

Ya ce irin waɗannan abubuwa na da illa ga lafiya, suna kuma lalata makomar matasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata