Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Comrade Shehu Sani, ya karyata ikirarin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, cewa Abubakar Idris wanda aka fi sani da Dadiyata ba mai sukar gwamnatin Kaduna ba ne.
Dadiyata, malami a Sashen Turanci da Ilimin Harshe na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, an sace shi a gidansa da ke Kaduna ranar 2 ga Agusta, 2019, kuma tun daga lokacin ba a sake jin duriyarsa ba ko fitar da cikakken bayani daga hukumomi.
A wata hira da El-Rufai ya yi a ARISE NEWS, ya ce Dadiyata ya fi sukar gwamnatin Kano ne da Abdullahi Ganduje, ba gwamnatin Kaduna ba. Sai dai Shehu Sani ya mayar da martani a shafinsa na X, yana cewa Dadiyata mai sukar gwamnatin Kaduna ne kuma mazaunin Kaduna.
Sani ya kuma ce tun bayan sace Dadiyata babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin Kaduna ko ziyarar ta’aziyya ga iyalansa, yana mai cewa iyalansa na nan a shirye su yi bayani ga duk mai neman gaskiya.
