Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya isa babban filin taro na Eagle Square domin halartar babban bikin zagayowar Ranar ‘Yan Sanda ta ƙasa na shekarar 2026.
Shettima, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi gaisuwar jami’an ‘yan sanda da ke faretin bude bikin, kamar yadda sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkowcha, ta bayyana.
Sanarwar ta ce, a lokacin da aka fara bikin, mataimakin shugaban ƙasar ya karɓi gaisuwar jami’an da aka jera a sahun faretin girmamawa.
Bikin ya haɗa manyan jami’an gwamnati, shugabannin rundunar ‘yan sanda, da sauran shugabannin tsaro, tare da jami’an ‘yan sanda daga sassa daban-daban na ƙasar.
Haka kuma, jaridar Punch an bayyana cewa a bikin an girmamawa gudumawar jami’an ‘yan sanda da suka rasa rayukansu yayin da suke bakin aiki domin kare al’umma.
An fara bikin ne da fareti da sauran shirye-shirye, inda jami’an ‘yan sanda suka cikin cikakken tsarin fareti domin tarbar mataimakin shugaban ƙasar a liyafar da aka shirya domin tarbarsa a taron na shekara-shekara.
