Jam’iyyar APC na tsara wata sabuwar dabara domin tabbatar wa Shugaba Bola Tinubu nasara a zaɓen 2027, ta hanyar ƙarfafa goyon baya a yankunan Kudu da Arewa ta Tsakiya, a daidai lokacin da wasu ƙungiyoyi a Arewa ke nuna rashin gamsuwa da gwamnatinsa.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, majiyoyi a cikin jam’iyyar sun ce an fara wannan shiri tun sama da watanni biyar da suka wuce, bayan rahotanni sun nuna yiyuwar turjiya daga wasu sassan Arewa da kuma haɗin gwiwar ’yan adawa. Sun ce manyan jiga-jigan APC ne ke jagorantar dabarar, da nufin kakkabe barazanar siyasa tun kafin 2027.
A cewar majiyar, APC na da niyyar tabbatar da cewa dukkan jihohin Kudu sun tsaya tsayin daka tare da Tinubu, tare da jingina da muhimmancin ƙuri’un Arewa ta Tsakiya, domin rage tasirin duk wata adawa da ka iya tasowa daga Arewa.
