Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika kudirin kasafin kudin jihar Ribas na Naira tiriliyan 1.48 ga majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi a wannan Alhamis.
Shugaban ya ce an yi kudirin kasafin saboda soke kasafin kudin jihar na 2025 da kotun koli ta yi da kuma ayyana dokar ta-baci a jihar.
Shugaban ya ce za a kashe bilyan 324 daga cikin kudin wajen samar da ababen more rayuwa, inda aka ware Naira biliyan 166 ga fannin kiwon lafiya, yayin da za a kashe biliyan 75.6 kan harkar ilimi da kuma biliyan 31.4bn bangaren noma.
