Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 16.7 domin sake...

Shugaba Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 16.7 domin sake gina gadar Mokwa da gaggawa

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da Naira biliyan 16.7 domin gina gadar Mokwa da ke Jihar Neja, wadda ambaliyar ruwa ta karya a watan Mayu.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya sanar da haka a Abakaliki ranar Asabar, bayan ganawa da Ministan Ayyuka, Dave Umahi.

Idris ya ce amincewar shugaban kasa ta nuna yadda gwamnati ke da saurin mayar da hankali ga matsalolin da suka shafi al’umma.

A nasa ɓangaren Umahi, ya bayyana Tinubu a matsayin shugaba wanda ke kula da bukatun jama’a, yana mai cewa amincewar ta nuna jajircewar gwamnati wajen magance matsalar al’umma a sassan ƙasar.

Baya ga Mokwa, Umahi ya ambaci wasu muhimman gine-ginen da aka amince da su a kwanakin baya, ciki har da gyaran gadar Wukari a Taraba, gadar Lokoja, hanyar Afikpo da ta hada Ebonyi da Abia da Imo, gadar Keffi, gadar Jebba a Kwara, gadaje bakwai a Edo da kuma gada a Jihar Kebbi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata