Wednesday, April 8, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu ya bayar da umarnin aikewa da karin sojoji da kayan...

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin aikewa da karin sojoji da kayan aiki don murkushe ‘yan ta’adda

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya sanar da umarnin shugaba Tinubu na tura karin sojoji da jirage marasa matuka domin kawo karshen’ yan ta’adda a fadin kasar.

 

Kashim Shettima ya bayyana haka ne cikin sakonsa na jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Borno, bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai yankin Darajamal da ke karamar hukumar Bama, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan sojoji da fararen hula.

 

Mataimakin shugaban kasar ya tabbatar wa da al’ummar cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da basu goyon baya a yakin da jihar ta Borno ke yi da matsalar tsaro.

 

Kazalika ya jaddada shirin gwamnatin shugaba Tinubu na duba yiwuwar kafa ‘yan sandan jihohi don kara daidaita lamuran tsaro a fadin kasar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata