Shugaban majalisar wakilai, Tajudden Abbas, ya ce shugaba Tinubu a shirye yake domin tabbatar da an gudanar da ingantaccen zabe a 2027.
Abbas ya fadi haka ne a wata tattaunawa da tawagar kungiyar kasashen Turai a Abuja a ranar Alhamis inda ya ce, majalisar kasa na kokari wajen ganin an yi ma dokokin zaben 2022 kwaskwarima biyo bayan korafe-korafe daga cikin gida da wajen bayan zaben 2023.
Hakazalika ya kara da cewa, tuni majalisun kasa suka fara kokarin kawo kudirin sauye-sauye domin karfafa dokokin zabe gabanin zabe mai zuwa
