Kwamitin shirya bikin ranar dimokuradiyya ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na kwamitin, ya ce Tinubu zai halarci zaman hadaka na majalisun dokokin kasar a ranar Alhamis.
Sai dai Adeoye ya ce ba za a yi Fareti ba kamar yadda aka saba a ranar dimokradiyya, sai dai za a gudanar da lakca kan bikin ranar dimokuradiyya a fadar shugaban kasa dake Villa.
