Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya umarci a janye Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills, tare da wasu ƙwararrun jakadu daga muƙamansu, a wani mataki da ake cewa na da nufin daidaita wakilcin diflomasiyyar Amurka da manufofin “America First.”
Rahoton Politico ya ce jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da cewa yawancin jakadun da abin ya shafa an naɗa su ne a zamanin tsohon shugaban ƙasa Joe Biden, kuma wa’adinsu zai ƙare nan da Janairu. An ce za su iya komawa Washington domin wasu ayyuka idan suna so.
Rahoton ya nuna cewa Afirka ce ta fi shafa, inda jakadu daga ƙasashe 13 ciki har da Nijeriya, Burundi, Kamaru, Côte d’Ivoire, Senegal da Uganda suka fuskanci janyewa. Haka kuma an shafi yankunan Asiya-Pasifik, Turai, Gabas ta Tsakiya, Kudancin Asiya da Latin Amurka.
A wata sanarwa, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce wannan al’ada ce a kowace gwamnati, tana mai jaddada cewa jakadu na aiki ne bisa yardar shugaban ƙasa, kuma hakki ne nasa ya zaɓi wakilan da za su aiwatar da manufofinsa na Amurka Farko.
